• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

WAEC Ta Kwace Lasisin Makarantu 574 Sakamakon Satar Amsa

by Abubakar Sulaiman
7 months ago
WAEC

Hukumar shirya jarrabawar  kammala Sakandire a Yammacin Afrika (WAEC) ta Nijeriya ta sanar da cewa ta kwace lasisin makarantu 574 da aka samu da laifin aikata maguɗi a jarrabawar.

Hukumar ta bayyana cewa waɗannan makarantu ba za su iya gudanar da jarrabawa ba, koda yake jarrabawar 2025 (WASSCE) kuma za a fara ta ne  daga Alhamis, 24 ga Afrilu, 2025.

  • Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Yi Aiki Tare Don Daidaita Mummunan Yanayi A Yankin Manyan Tabkuna Na Afirka
  • WAEC Ta Samar Da Hanya Mai Sauri Wajen Sake Zana Jarrabawar WASSCE Ga Ɗaliban Da Suka Yi Tuntuɓe 

Shugaban Ofishin WAEC na Nijeriya, Dr. Amos Dangut, ya bayyana hakan a cikin wani taron manema labarai a ranar Alhamis a shalƙwatar hukumar da ke Legas. Dangut ya ce WAEC ta tura jerin sunayen makarantu da aka soke lasisin su zuwa ga gwamnatin tarayya. Ya ƙara da cewa, wannan mataki ya shafi dukkanin cibiyoyin jarrabawa, inda aka tabbatar da cewa ba za a gudanar da jarrabawa a cikin waɗannan makarantu ba.

Dangut ya bayyana cewa adadin ɗaliban da suka yi rijista don rubuta jarrabawar WASSCE ta 2025 ya kai 1,973,253 daga makarantu 23,554, inda 979,228 daga cikinsu suka kasance maza, 994,025 kuma mata.

Ya kuma bayyana cewa hukumar tana amfani da fasaha wajen inganta gudanar da jarrabawar, wanda ya haɗa da gabatar da jarrabawar WASSCE na kwamfuta (CB-WASSCE) na farko. Dangut ya ƙara da cewa wannan mataki na kawo canji yana daga cikin ƙoƙarin tabbatar da nagarta da gaskiya a cikin tsarin ilimi.

LABARAI MASU NASABA

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu
Ilimi

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

November 8, 2025
gombe
Ilimi

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Ilimi

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
Next Post
Yawan Kudaden Da Al’ummun Sin Suka Kashe Kan Kayayyakin Masarufi Ya Kai Yuan Triliyan 12.5 A Rubu’in Farko

Yawan Kudaden Da Al’ummun Sin Suka Kashe Kan Kayayyakin Masarufi Ya Kai Yuan Triliyan 12.5 A Rubu’in Farko

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.