Masana’antar shirya fina-finan Nijeriya ta yi shura wajen shirya manyan fina finai masu nishadantarwa, fadakarwa da kuma wa’azantarwa, fina finan kudancin Nijeriya sun fara ne daga karamar masana’anta har ta kai ga zama babbar cibiyar duniya da muka sani a yau a matsayin Nollywood, hakazalika Kannywood wadda ta kasance gishiri cikin miyar masana’antar nishadi da al’adu ta nahiyar Afirika a halin yanzu.
Yayin da masana’antar ke ci gaba da fitar da sabbin jarumai masu hazaka da suka kafa tarihin zama wani madubi ga yara masu tasowa, har yanzu tabon rashin wasu fitattun fuskoki bai gushe daga zuciyar babbar masana’antar ta nishadi ba, a wani yanayi da za a iya kira na juyayi jaruman sun wuce sun bar wani wagegen gibi wanda ba lallai bane a samu wani jarumi da zai iya cikawa ba.
- Kwararru Sun Yi Musayar Ra’ayoyi Dangane Da Wayewar Kan Sin Da Afirka
- Fursunoni 62 Sun Rubuta Jarrabawar NECO da MBAIS A Kano
A wannan mako LEADERSHIP Hausa ta zakulo wasu fitattun fuskokin jaruman manyan masana’antun nishadi na Nollywood da Kannywood da su ka kwanta dama, da ba za a taba iya mantawa da gudunmawar da su ka bayar ga masana’antar ba.
1. Sam Loco Efe
Fitaccen jarumi Sam Loco Efe jarumin barkwanci ne a Nijeriya da aka haifa ranar 25 ga watan Disamba a shekarar 1945, a Jihar Enugu, ya girma a Abakaliki, Jihar Ebonyi, tarihin Sam a wasan kwaikwayo ya fara ne a cikin wasan kwaikwayon “Langbodo” a lokacin FESTAC ’77, inda a nan ne aka gane irin tarin baiwar da yake da ita a bangaren wasan kwaikwayo, Loco ya saka sunashi a cikin jerin sunayen fitattun ‘yan wasan Afirka.
Loco ya shafe tsawon lokaci a wannan bangaren da kuma wasannin talabijin kamar “Hotel de Jordan” da kuma fina-finan Nollywood da yawa, kwarewarshi a harshen Ingilishi ya sa galibi yake isar da sakonni masu rikitarwa ga masu kallo ba tare da wahala ba, masu sharhi sun taba bayyana shi a matsayin “Dan wasan Nollywood mafi hazaka da ya taba rayuwa a Duniya, Sam Loco Efe ya rasu ne a ranar 7 ga Agusta, 2011, yana da shekaru 65 a duniya.
2. Rabilu Musa (Ibro)
Rabilu Musa wanda aka fi sani da Dan Ibro, fitaccen jarumin barkwanci ne kuma jarumi a masana’antar fina-finan Kannywood, an haife shi a ranar 12 ga Disamba, 1971, a garin Danlasan na jihar Kano, ya fara karatunsa a makarantar firamare ta Danlasan, daga nan kuma ya halarci Kwalejin Malamai ta Gwamnati da ke Wudil, a shekarar 1991, ya shiga aikin kula da gidajen yari na Nijeriya, inda ya yi aiki kafin ya fara wasannin barkwanci.
Fim din Dan Ibro na farko mai suna “Yar Mai Ganye” ya nuna yadda Ibro ya yi fice a fagen barkwanci, salon sa na musamman da barkwancinsa ya na burge masu kallo, wanda hakan ya sa ya yi suna a arewacin Nijeriya, a tsawon shekaru, ya fito a fina-finai da dama, da suka hada da “Ibro Dan Almajiri”, “Ibro Police”, da “Ibro Dan Fulani”.
A tsawon rayuwarsa, Dan Ibro ya samu yabo da dama saboda gudunmawar da ya bayar a harkar fim, musamman ma, an karrama shi da lambar yabo ta Best Comedian award a Kannywood Awards 2015, Rabilu Musa ya rasu ne a ranar 9 ga watan Disamba, 2014, yan kwanaki kadan ya cika cika shekaru 43 a duniya, mutuwar sa ta bar gibi sosai a Kannywood.
3. Justus Esiri
Justus Esiri fitaccen dan wasan Nijeriya ne, an haife shi a ranar 20 ga Nuwamba, 1942, a Oria-Abraka, jihar Delta, ya halarci kwalejin Urhobo da ke Effurun kafin ya koma Jamus don ci gaba da karatu, a can ya yi karatu a cibiyoyi daban daban, ciki har da Jami’ar Madimilian a Munich inda ya kamu da sha’awar wasan kwaikwayo, Justua ya fara harkar wasan kwaikwayo a Jamus, inda ya yi wasa a tsakanin 1968 zuwa 1969.
Da ya dawo Nijeriya, Justus ya yi suna saboda rawar da ya taka a cikin fitaccen shirin talabijin mai suna “The Billage Headmaster”, inda ya fito a matsayin shugaban makaranta, a tsawon shekarun aikinsa, ya fito a cikin fina-finai da shirye-shiryen Talabijin da dama, ciki har da “Wasted Years”, “Foreber”, da “Coridors of Power”, ya sami lambobin yabo da yawa, ciki har da kyautar mafi kyawun jarumi a bikin karramawa ta 9th Africa Mobie Academy Awards saboda rawar da ya taka a “Assassins Practice”, Gwamnatin Nijeriya ta kuma karrama shi da mukamin Officer of the Order of the Niger (OON), Justus Esiri ya rasu ne a ranar 19 ga Fabrairu, 2013, a Legas bayan fama da cutar ciwon suga.
4. Hajiya Zainab Booth
Hajiya Zainab Musa Booth ta kasance fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina-finan Kannywood, an haife ta a shekarar 1960, mahaifiyarta Bafulatana inda kuma mahaifinta ya kasance dan kasar Scotland, wannan ya matukar taimakawa basirar da Zainab takeda ita a harkar fim ta hanyar nuna mabanbantan al’adu da zamantakewa da ta koya a wajen iyayenta da suke a mabanbantan kabilu, wanda hakan ya sa mafi yawancin masu kallo a duk fadin arewacin Nijeriya ke son ta.
Bayan aikin wasan kwaikwayo, Zainab ta kasance uwa ga ‘ya’ya hudu, ciki har da fitattun jaruman Kannywood Maryam Booth da Amude Booth, Zainab Booth ta rasu ne a ranar 1 ga Yuli, 2021, tana da shekaru 61, bayan gajeruwar rashin lafiya inda aka yi jana’iizarta a birnin Kano, Al’ummar Kannywood sun yi alhinin rasuwar ta.
5. Bukky Ajayi
An haifi Bukky Ajayi a ranar 2 ga watan Fabrairu, 1934, ta yi karatun sakandare a Ingila inda ta samu tallafin karatu na gwamnatin tarayya, bayan ta yi shekaru shida a kasar waje, ta dawo Nijeriya a shekarar 1965, ta fara aikin gabatar da shirye-shirye da labarai a gidan talabijin na Nijeriya (NTA) a shekarar 1966.
Tarihin wasan kwaikwayon Bukky ya fara ne da shirin talabijin na “Billage Headmaster” a cikin shekarun 1970, wanda ya sa ta zama sananniya a yawancin gidajen Nijeriya, a tsawon rayuwarta ta fito a cikin fina-finai da yawa, ciki har da “Diamond Ring”, “Witches”, da “Thunderbolt”, don karrama gagarumar gudunmawar da ta bayar a Nollywood, Bukky ta sami lambar yabo ta Africa Magic Biewers Choice Awards a shekarar 2016, Bukky Ajayi ta rasu a ranar 6 ga Yuli 2016, tana da shekaru 82 a duniya.
6. Saratu Gidado
Ita dai Saratu Gidado, an haife ta a Jihar Gombe, a ranar 17 ga watan Janairu 1968, ta yi karatu tun daga matakin firamare a Jihar Kano, Daso, wadda tayi suna wajen fitowa a matsayin “Ba Sani Ba Sabo” a shirye shiryenta, ta kasance abar so a wajen masu kallo saboda yadda take yin abu da gaske kuma babu tsoro a cikin Shirin Fim, Daso ta yi suna ne musamman wajen fitowa a matsayin mara tsoro kuma masifaffiya, hakan ya sa ta fita daban a cikin ragowar jarumai mata a masana’antar saboda ta na iya fitowa a duk yanayin da ake bukata ta fito musamman a matsayin uwa mai tsoratarwa.
A shekara ta 2000 ta tsunduma harkokin fina finan hausa, inda ta fara fitowa a cikin Shirin “Linzami Da Wuta” wanda kamfanin Sarauniya ya shirya, wasu daga cikin fina finan da ta fito sun hada da “Yar Mai Ganye”, “Nagari”, “Fil’azal” da kuma Shirin turanci na “There is Way” da kamfanin Jammaje ya shirya, a shekarar 2016 ne Sarkin Kano na 14 Muhammad Sanusi II ya nada ta a matsayin Jakadiya, kamar yadda iyalai da yan uwanta suka bayyana, ta rasu da safiyar Talata 9 ga watan Afrilu na shekarar 2024.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp