Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kira Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, tare da mambobin kwamitin hukumar wani taro na musamman.Â
Za a gudanar da taron ne yau da ƙarfe 1:30 na rana a Ɗakin Taro na Mataimakin Shugaban Ƙasa.
- 2027: Fastocin Takarar Shugaban Ƙasa Na Gwamnan Bauchi Sun Bayyana
- Tinubu Ya Komo Nijeriya Bayan Ziyarar Mako 3 A Turai
Wata wasiƙa da jaridar Daily Trust ta gani, wadda Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa manufar taron ita ce jin bayanai kan shirye-shiryen aikin Hajjin 2025 da kuma wasu matsaloli da ba a warware ba.
A cikin wasiƙar, an umarci shugaban NAHCON da ya halarci taron tare da dukkani mambobin hukumar, sannan ya zo da taƙaitaccen rahoto kan matakin shirye-shiryen hajjin bana.
An samu rikici a hukumar tun bayan da wasu mambobin kwamitin suka koka cewa ana watsi da su wajen yanke muhimman shawarwari da suka shafi shirye-shiryen hajjin bana.
Wannan ya kai ga aike ƙorafi zuwa ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.
A baya, Shettima ya gargaÉ—i shugaban hukumar da ka da ya ci gaba da tafiyar da NAHCON tamkar mallakarsa ce shi kaÉ—ai.
Sai dai shugaban ya musanta zarge-zargen, inda ya bayyana cewa bai aikata komai ba da ya saɓa wa doka ko tsarin aikin hukumar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp