Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a jiya Talata cewa, a yayin da ake ci gaba da samun karuwar cin zarafi daga bangare guda, ya kamata kasar Sin da Birtaniya su kiyaye tsarin kasa da kasa da aka kafa bayan yakin duniya na biyu.
Wang ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen Birtaniya David Lammy, inda ya ce, bangarorin biyu suna dauke da nauyin yin riko da tsarin kasa da kasa karkashin MDD, da kuma kare tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban.
- Dalilin Da Zai Iya Hana Ni Sake Bugawa Manchester United Wasa – Rashford
- Sabbin Haraji: Yadda ‘Yan Bindiga Ke Tilasta Wa Jama’a Biyan Miliyoyin Kuɗi A Zamfara
Wang ya kara da cewa, tun daga farkon wannan shekara, an yi nasarar gudanar da taron tattaunawa kan tattalin arziki da hada-hadar kudi na Sin da Birtaniya, da tattaunawa kan manyan tsare-tsare, da tattaunawa kan makamashi. Kana kuma ana ci gaba da shirye-shiryen kara yin tattaunawa a fannonin da suka hada da kirkirarriyar basira ta AI, da kimiyya da fasaha, da sauyin yanayi, da ilimi, da tattalin arziki da cinikayya.
A nasa bangaren, Lammy ya bayyana farin cikin Birtaniya game da yadda ake samun kyakkyawan ci gaba a dangantakar kasashen biyu. Ya kuma kara da cewa, Birtaniya a shirye take ta kara habaka musaya mai inganci daga dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu, da yin shawarwari tare da kasar Sin a kai a kai kan batutuwan bangarorin biyu da na bangarori daban daban wadanda suka shafi moriyar kasashen biyu, tare da tinkarar kalubale tare.
A wannan rana har ila yau, Wang ya kuma tattauna ta wayar tarho da ministar harkokin wajen Austria Beate Meinl-Reisinger bisa bukatarta. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp