Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ratba hannu kan dokar da ta amince a yanke hukuncin kisa kan duk wanda aka kama a jihar a matsyin dan bindiga, satar shanu da aikata ayyukan Kungiyar asiri ko kuma masu bayar da bayanan sirri ga masu garkuwar da mutane.
Gwamnan ya bayyana haka ranar Talata.
Ya ce, a ranar 28 ga watan Yunin wannan shekara, na gabatar da kuduri kan haramta ayyukan ‘yan Bindiga, sace mutane, satar shanu, aikata ayyukan asiri.
- Zunzurutun Ma’adanai: Nijeriya Na Iya Zama Mafi Kyawun Wurin Zuba Jari A Duniya – Minista
- Gwamnatin Tarayya Ba Ta Muhimmanta Tsaro Ba – Matawalle
Daga yanzu duk wadanda aka kama a jihar da aikata wadannan laifukan, hukuncin su sh ine kisa.
Matawallen ya kara da cewa, duk wadanda aka kama na goyon bayan masu aikata wadannan laifukan a jihar, za a yanke musu hukuncin zama a gidan gyara hali har tsawon rayuwa ko zaman gidan gyaran hali na shekaru 20 ko na shekaru 10 ba tare da tara ba.
Gwamnan ya kuma umarci Jami’an tsaro a jihar da su fara bi gida-gida a masarautu 19 da ake da su a jihar don su bankado masu aikata manyan laifuka.
Gwamnan ya kuma sanar da takaita zirga-zirgar babura a yankunan birnin Jihar da wajen jihar daga karfe 9 na dare, ya kuma ba Jami’an tsaro umarnin harbe duk masu sana’ar Achaba da suka karya wannan umarnin.