Ranar: 03-10-1949
Dokta Nnamdi Azikiwe (wanda aka fi sani da Dr Zik), mutumin da ya ki yin gazawa da watsi da fafutukar neman ‘yancin kai, ya sake komawa Landan domin yakin neman ‘yancin gida Nijeriya, kasar da ke yammacin Afirka da ke karkashin mulkin Birtaniya tun 1866.
Dokta Zik, mai shekaru 45, yana da tsayin ƙafa sosai, ya tabbatar a cikin ransa tafiyar da ya yi a 1947 za ta kasance ita ce ziyararsa ta ƙarshe zuwa Ofishin Mulkin Mallaka, a kokarin da yake da fafutukar neman ‘yancin kai ga ƙasarsa.HOTO NA:- Dr NNAMDI AZIKIWE (Dr ZIK) suna tafiya akan titin birnin Landan tare da Ahmed Mahmud Saad Zungur, sakataren gwamnatin tarayya na majalisar tarayyar Nijeriya da Kamaru.
Ahmed Mahmud Saad Zungur (1915 – 1958) ɗan siyasan Nijeriya ne kuma mawaƙi wanda yana cikin malaman farko a Arewacin Nijeriya da suka yi kira da a gyara al’uma ta hanyar ilimi a lokacin mulkin mallaka.
📸: Tarihin Igbo