Mazauna a sassa daban-daban na Jihar Zamfara na fama da yadda ‘yan bindiga ke tatsar kudade daga hannunsu da yawansu ya kai maguden miliyoyin naira muddin suna son zama cikin kwanciyar hankali a gidajensu, kamar yadda bincike ya nuna.
‘Yan bindigan na tursasa wa mutane biyan harajin ne da barazanar za su yi garkuwa da su, ko kisa ko barnata gari, lamarin da ke sanya wa mutanen firgici da tashin hankali inda suke zaban biyan kudaden domin zaman lafiya.
- Dattawan Arewa Sun Zargi Tinubu Da Nuna Wariya A Nade-Naden Mukamai
- Kudaden Da Ke Hannun Mutane Sun Ragu Zuwa Naira Tiriliyan 5 – Rahoto
Tun daga watan Janairun 2025, an tattaro cewa samar da naira miliyan 500 ne al’ummomin kauyuka suka biya kungiyoyin barayin daji daban-daban a kokarinsu na kauce wa kawo musu hare-hare.
A watan Janairu kawai, marigayi shugaban ‘yan fashin daji, Isuhu Yellow, ya sanya harajin naira miliyan 172.7 a kauyuka 25, ciki har da bukatar amfanin gona.
A misali, an kakaba wa kauyen Gijinzama harajin naira miliyan 8.5, Dakolo naira miliyan 5 da buhunan wake 20, da Kibari, Kunchin Kalgo naira miliyan 20, Sungawa naira miliyan 15, da Yalwa naira miliyan 2.7, da dai sauransu.
Ba da jimawa ba, wani shugaban ‘yan fashin dajin nan, Dogo Gide, ya bukaci a biya naira miliyan 100 daga wasu al’ummomi 23 da ke karamar hukumar Tsafe, lamarin da ya sa jama’a suka kauracewa gidajensu.
Al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Kunchin-Kalgo da aka nemi naira miliyan 20 daga wajensu, Sungawa naira miliyan 15, Rakyabu naira miliyan 15, da Kwaren Mai-Saje naira miliyan 10.
A ranar Lahadi, 20 ga Afrilu, ‘yan bindiga sun sake neman naira miliyan 60 daga mazauna kauyen Dankurmi a karamar hukumar Maru.
Wani mazaunin kauyen Kwalfada a karamar hukumar Tsafe wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya tabbatar da cewa ‘yan garkuwa da mutanen sun kakaba wa rayuka da dama haraji a yankin.
Ya ce, miliyoyin naira ne masu garkuwan suka nema a hannun jama’a ko kuma su kawo musu farmaki.
Wani mazaunin kauyen Dan Jibga, Mai suna Muhammad Dogo, ya ce ‘yan fashin daji sun sanya harajin naira miliyan 10 ga al’ummar Gama Lafiya bayan kashe wasu mutum biyu a ranar Lahadi da Litinin.
Dogo ya ci gaba da cewa, sauran kauyukan da harajin ya shafa sun hada da Unguwar Tofa naira miliyan 26.6, Makera naira miliyan 15, Sungawa naira miliyan 20, Rakyabu naira miliyan 7, Yalwa naira miliyan 8, Kwarin Mai Saje naira miliyan 11, Langa-Langa, inda harajin ya kai tsakanin naira miliyan 20 zuwa naira miliyan 30.
Ya kara da cewa ‘yan fashin dajin sun kwace kauyukan Gidan Dawa, Rijiyar Tsakar Dawa, Dan Jibga, da Bilbis.
Wani mazaunin garin Mara da ke karamar hukumar Maru, Malam Ibrahim Maru, ya koka da yadda matsalar ‘yan fashin dajin ke ta kara ta’azzara a yankin Maru a ‘yan kwanakin nan.
Ya ce, “Hanyar Talata Mafara zuwa garin Maru ta zama tarkon mutuwa ga matafiya da direbobin wanda sun daina amfani da hanyar bayan karfe 4 na yamma.
“Da zarar karfe 4 na yamma ya yi zai yi wuya a samu direban da ke son daukar fasinjoji daga Maru zuwa Talata Mafara, kwanan nan na yi tattaki daga Talata Mafara zuwa Maru domin ziyarar jaje, amma da isa Maru, sai aka ba mu shawarar mu koma.
“Wannan hanyar ba ta da tsaro, ‘yan bindiga sun ci gaba da ayyukansu, suna gudanar da ayyukansu ba dare ba rana, sun yi garkuwa da mutane da dama, ciki har da mata da yara, a kauyuka daban-daban, kuma suna sanya haraji a kan al’ummomi da dama.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp