Kasar Sin ta cimma nasarar harba sabon tauraron dan’adam na ayyukan sadarwa mai suna Tianlian II-05, daga tashar harba kumbuna ta Xichang dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar.
An harba tauraron ne da karfe 12 saura mintuna 6 na tsakar daren jiya Lahadi agogon Beijing, ta amfani da rokar Long March-3B, kuma tuni ya shiga da’irarsa kamar yadda aka tsara.
Tauraron zai rika samar da hidimomin musayar bayanan sadarwa ga kumbunan sama jannati, irin su kumbuna masu dauke da ‘yan sama jannati, da tashar binciken sararin samaniya, domin nasarar ayyukan taurarin dan’adam marasa nisa da doron duniya, da taurarin dan’adam masu taimakawa aikin harba kumbuna.
Wannan ne karo na 572 da aka yi amfani da roka samfurin Long March wajen harba tauraron dan’adam na Sin zuwa samaniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














