Duk da bai wuce ƙasa da shekaru biyu ya kammala wa’adin mulkinsa ba, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da naɗin sabbin hadimai 173.
Sabbin naɗe-naɗen sun haɗa da: manyan hadimai na musamman guda shida, manyan hadimai guda 60, hadimai na musamman guda 38, da kuma wasu hadimai 63.
- Nijeriya Na Ke Yi Wa Biyayya Ba Wani Ko Jam’iyya Ba – El-Rufai
- Sojoji Sun Ceto Mutum 50 Da Aka Sace, Sun Ƙwato Shanu 32 A Katsina
Yawancin sabbin hadiman za su riƙa aiki ne a fannonin siyasa, hulɗa da jama’a, batutuwan fansho da na ma’aikata.
Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Mohammed Gidado, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Bauchi.
Gidado, ya ce naɗin hadiman na da nufin kawo sabbin dabaru a cikin gwamnati tare da tabbatar da cewa gwamnati tana wakiltar buƙatu da muradun al’ummar Jihar Bauchi.
Ya bayyana sabbin hadiman a matsayin ƙwararru masu gogewa a fannoni daban-daban na shugabanci da siyasa.
Ya ƙara da cewa an zaɓi sabbin hadiman ne bisa cancanta, kuma an ɗora musu nauyin tabbatar da tsarin mulki da ya fi mayar da hankali kan jama’a.
Gwamna Bala Mohammed ya taya su murna tare da kira a gare su da su ɗauki sabbin muƙamansu a matsayin hanya ta hidimta wa jama’a, su kasance masu jajircewa da biyayya wajen cika burinsa na ci gaban jihar da inganta ayyukan gwamnati.
“Wannan gwamnati ta ƙudiri aniyar ɗorewa da nasarorin da aka cimma ta hanyar gina kyakkyawan tarihi na shugabanci nagari da haɗin kai,” in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp