Darajar cinikayyar ba da hidima ta kasar Sin ta karu sosai, inda ta kai yuan triliyan 1.97 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 270 a rubu’in farko na bana, karuwar kashi 8.7 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.
Darajar jimillar hidimar fice ta kai yuan biliyan 835.15, karuwar kashi 12.2 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, yayin da darajar hidimar shige ta kai yuan triliyan 1.139, wanda ta nuna karuwar kashi 6.2 cikin dari.
Hidimomin tafiye-tafiye sun nuna karuwa mafi sauri na kashi 21.8 cikin dari. (Mohammed Yahaya)