Kwanaki 100 bayan kama aiki, Donald Trump da ajandarsa ta ba Amurka fifiko gaba da komai, sun shiga cikin matsala. A watannin Fabrairu da Afrilun bana, kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar da wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a, wadda ta mayar da hankali kan mutane 15,947 a fadin kasashe 38. Nazarin ya gano cewa, yanayin gamsuwa da ayyukan Trump daga masu bayar da amsa a Amurka, ya ragu sosai. Kuma manufar ba Amurka fifiko da ake amfani da ita a huldar kasa da kasa, ta sa masu bayar da amsa daga kasashe aminan Amurkar da ma kasashe masu tasowa ganin cewa, ba za a samu kyakkyawar makomar alakar kasashensu da Amurka ba. Sabuwar gwamnatin ta Amurka na fuskantar rashin aminci daga kasa da kasa.
Alkaluma sun nuna cewa, kaso 48.9 na Amurkawa da suka bayar da amsa a nazarin sun bayyana rashin gamsuwa da kamun ludayin sabuwar gwamnatin. Daga cikinsu, kaso 53.1 sun soki manufar ramuwar haraji dake ba da mummunan tasiri kan kasuwar hannayen jari ta kasar. Kaso 60.4 kuma, sun yi ammana cewa, manufofin tattalin arziki na cikin gida, ba gazawa wajen takaita hauhawar farashi kadai suka yi ba, har da kara hauhawar farashi, kana kaso 54 na kokwanto kan manufar matakin kudin ruwa na kasar.
Manufar ba Amurka fifiko ta jefa duniya cikin rudani, inda ta lalata aminci da kwarin gwiwar dake akwai tsakanin kasar da kawayenta. Alkaluma sun nuna gagarumin sauyi daga mutanen Australia da suka bayar da amsa a nazarin, inda kaso 65 ke ganin babu wata kyakkyawar makoma a dangantakar Amurka da Australia, adadin da ya karu maki kaso 24.5, idan aka kwatanta da nazarin da aka yi a baya. Haka ma kaso 55 na masu bayar da amsa daga kasar Italiya suka bayyana, adadin da ya karu da kaso 21.5 kan na nazarin da aka yi a baya. A Faransa da Jamus da Canada da Japan da Korea da Kudu, sama da kaso 70 na masu bayar da amsa ba sa ganin akwai kyakkyawar makoma dangane da dangantakar kasashensu da Amurka. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp