A yau Laraba ne ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wani takardar aiki mai taken “Rigakafin Covid-19, dakilewa da gano asalinsa: Matakai da matsayar kasar Sin.”
Baya ga babin gabatarwa da kuma na karshen, takardar ta kunshi babi uku, da suka hada da babin “Ba da gudummawar hikimar Sinawa ga nazarin asalin SARS-CoV-2,” da “Gudummawar da Sin ta bayar ga duniya game da yaki da Covid-19,” da kuma “Rashin martani mai kyau na Amurka game da annobar ta Covid-19.”
A cewar takardar, cututtuka masu yaduwa abokan gaba ne na ‘yan Adam. Kuma duk wani yunkurin siyasantar da matakan kimiyya game da yaki da cututtuka masu yaduwa, ko ma kirkirar bayanan karya don kai hari ga wasu kasashe don muradun kansu, tabbas zai saka lafiya da jin dadin dukkan ’yan Adam cikin hadari, ciki har da nasu. Kasar Sin za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da sauran kasashen duniya wajen sa kaimi ga bunkasa da gudanar da harkokin kiwon lafiyar jama’a a duniya, da kara himma da ba da gudummawa don hana bullar sabbin cututtuka masu yaduwa a nan gaba. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp