Da yammacin jiya Talata, wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya gana da jakadan Philippines dake kasar, don tattaunawa game da mummunan ayyukan da bangaren Philippines ya yi a kwanakin baya da suka shafi yankin Taiwan na Sin da ma harkokin tsaro. Wannan mataki da Sin ta dauka ba kawai ya kare halastaccen hakkinta da moriyarta ba, har ma ya kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Tun lokacin da gwamnatin Philippines mai ci ta hau karagar mulki, ga dukkan alamu tana son nuna karfinta ta yin amfani da karfin wasu kasashe. Philippines ta yi amfani da tekun kudancin kasar Sin a matsayin wata hanya ta jan “hankali” da samun “tausayawa”, tana kokarin yin amfani da goyon bayan da wasu kasashe suka ba ta ta fannin bayanan sirri da diflomasiyya da sauransu, don neman cimma burinta da bai dace ba na fadada yankunanta da ma iyakokin teku.
- Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
- Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga , Sun Ceto Fasinjoji 6 A Taraba
Sai dai kuma, tuni sassan kasa da kasa sun gano makircinta. Da Amurka da Japan duk sun taba kafa mulkin mallaka a Philippines, don haka taimako da goyon baya da suke nunawa Philippines a yau, ba komai ba ne illa yunkurin kare moriyar kashin kansu.
A ko da yaushe Sin tana himmatuwa wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, tare da kira da a warware rikici ta hanyar tattaunawa. A sa’i daya kuma, aniyarta ta kiyaye ikon mulkin kasa, da hakki da moriyarta a tekun kudancin Sin ba za ta sauya ba. Ita kasar Philippines kuma za ta dandana kudarta bisa ga yadda ta aiwatar da mummunan mataki kan batun zirin tekun Taiwan, da nufin biyan bukatun Amurka game da dabarunta a yankunan tekun Indiya da na fasifik. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp