Babbar Kotun da ke da zamanta a jihar Adamawa, ta yanke wa wani fitataccen Dan damben gargajiya mai suna Thank-You Grim da ke zaune a yankin Silli cikin karamar hukumar Guyuk hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa zargin hallaka matarsa.
An gurfanar da shi ne a gaban kotun da Mai Shari’a Alkali Nathan Musa ke jagoranta a kan tuhuma daya ta kisan a karkashin doka ta 192 (b) a cikin baka ta jihar Adamawa ta shekarar 2018.
Alkali Nathan Musa a lokacin da yake yanke hukuncin ya ce, dan sanda mai gabatar da karar ta tabbatar wa da kutun hujojin cewa, Grim ya aikata laifin a saboda hakan kotun ta yanke wa dan damben hukuncin kisa ta hanyar raya.
Dan sanda mai gabatar da karar ya sheda wa kotun cewa, Grim ya kashe matarsa ta hanyar maka ta da kasa, inda daga bisani ya rabka mata wani karfe a kai inda Hakan ya janyo mutuwar ta a ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2018.
An ruwaito cewa, ma’urantan suna zaune a waje da ban da ban tun watan Janairun shekarar 2018 bayan an gaza sasanra su.
Bayan da mariganyiyar ta samu wani da za sake aura, ta bukaci Grim ya ba ta takardar saki, inda hakan ya harzuka Grim.
Bugu da kari, an ruwaito cewa, maimakon Grim ya amince da wannan bukatar ta mariganyiyar mai suna Kwalla, sai ta gayyace da ta zo gidansa ta karbi takardar ta saki amma sai ya rike ta da dawo su ci gaba da zama a matsayin miji da mata amma taki amince wa da bukatarsa, inda rikici ya kaure a tsakanin su har kwada mata karfen inda hakan ya yi sanadiyar mutuwar ta.