A yau Jumma’a, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a halin yanzu kasar tana nazarin halin da ake ciki, yayin da a baya-bayan nan Amurka take tuntuba ta hanyoyin da suka dace masu yawa, inda take bayyana muradin hawa teburin tattaunawa da kasar Sin kan batutuwan karin harajin kwastam.
Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayyar Sin ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, kasar Sin tana nan a kan bakanta game da matsayin da ta dauka kan wannan batu, watau idan aka tilasta mata yaki kan lamarin, za ta sha damarar gwabzawa har sai ta ga abun da ya ture wa buzu nadi, kana idan aka zabi hawa teburin tattaunawa, to, kofarta a bude take.
- FIRS Ta Umarci Bankuna Su Rufe Asusun Ajiyar Tara Harajin Da Ba Su Cika Ka’ida Ba
- An Cafke Saurayi Bisa Zargin Yi Wa ‘Yar Budurwarsa Fyade A Bauchi
Sanarwar ta kuma ce, yakin karin harajin kwastam da na cinikayya, Amurka ce ita kadai ta kaddamar da yi, kuma idan har tana son a tattauna, tilas ne ta nuna da gaske take yi ta hanyar yin shirye-shirye da kuma daukar kwararan matakai, kamar su gyara kura-kuran da take tafkawa, da kuma soke karin harajin da ta yi ita kadai tsiga-tsiyau.
Ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta lura da yadda Amurka ke ta faman magana a-kai-a-kai game da gyare-gyare kan matakan harajin da ta dauka. Jami’in ya ce, “A duk wata tattaunawa ko shawarwari da za a yi, idan har Amurka ba ta gyara kuskurenta na matakan harajin da ta dauka ita kadai ba, to hakan zai nuna rashin gaskiyarta, da kuma kara kawo cikas ga amincewa da juna.”
Mai magana da yawun ma’aikatar ya jaddada cewa, wayon da ake nunawa na abin da ake fada daban, wanda ake aikatawa daban, ko ma yunkurin amfani da tattaunawa don a fake da guzuma a harbi karsana da kuma cin zarafi ko shafa kashin kaji, ba zai yi tasiri a kan kasar Sin ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp