Jam’iyyar PDP da ke mulki a Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa bisa kyawawan ayyuka da gwamnatin jihar ke shimfidawa wanda al’ummar jihar suka gamsu da su tare kuma kyakkyawar hadin kai da ke tsakanin mambobin jam’iyyar a jihar, babu wani dalilin da zai sanya wasu su ma ji sha’awar ficewa daga jam’iyyar.
Jam’iyyar ta tabbatar da cewa kan mambobinta da shugabanninta a hade suke wanda hakan ne zai tabbatar da irin nasarar da jam’iyyar za ta samu a zaben 2027 da ke tafe.
- Bayan Fara Binciken $2.96bn, An Samu N80bn A Asusun Tsohon Daraktan Kamfanin NNPCL
- Dakataccen Gwamnan Ribas Ya Dawo Daga Hutun Makonni Biyu A Kasar Waje
Sakataren watsa labarai na jam’iyyar a matakin Jihar Bauchi, Dakta Dayyabu Chiroma ya shaida wa LEADERSHIP a hirarsa da wakilinmu cewa jam’iyyar za ta samu gagarumin nasara a dukkanin kujeru a jihar sakamakon hadin kai da ayyukan da suke gudanarwa.
“Ka san idan za ka yi la’akari da sauran jihohin da suke barin jam’iyyarsu su shiga wata jam’iyya ni a tunanina tsoro ne karawa da babban jam’iyyar adawar da ke jihar ba, yanzu misali a Jihar Delta shi gwamnan jihar ya san daker ya ci zabe a 2023 sannan kuma yana da yakinin idan bai fita daga PDP ya shiga APC ba ba zai iya samun nasara a 2027 ba; to mu in ka yi la’akari da hakan a jam’iyyar mu ta PDP a Jihar Bauchi tun da ake mulki sau daya APC ta samu galba a 2015 sakamakon maja wanda ya ci ko’ina. “Duk gwamnonin PDP da aka yi a Jihar Bauchi ba wanda bai kafa tarihin yin kyawawan ayyuka ba. Idan za ka kwatanta mulkin Ahmad Muazu da Dakta Malam Isa Yuguda ba za ka taba kwatantawa da abun da shi M.A Abubakar ya yi ba, kowa ya sani mulkin APC wanda M.A Abubakar ya yi ba a taba mummunar mulki irinta ba.
“Balle kuma yanzu da gwamna Bala Muhammad Abdulkadir ke gudanar da kyawawan ayyuka da kawo ci gaba da kyautata wa jama’a da inganta fannoni daban-daban wanda al’ummar jihar gaba daya sun yi gamsu da kokarinsa ba wani dalilin da wani zai ji sha’awar ficewa daga jam’iyyar.”
Ya nuna cewa duk da matsalolin da jam’iyyun siyasa ke fuskanta a Nijeriya bai takaita ga PDP zalla ba, amma ba su ji dadin yadda wasu fitattun mutane ke ficewa daga jam’iyyar ba ciki har da gwamnan jihar Delta, da tsohon gwamnan da ‘yan majalisu tarayya da na jihohi, da shugabannin kananan hukumomi a ce sun bar jam’iyyar PDP ba karamin rashi ba ne.
Sai dai ya tabbatar da cewa wannan matakin ba zai shafi nasarar da jam’iyyar ta saba samu a jihar Delta ba, ya tabbatar da cewa PDP ce za ta yi nasara a Delta a zaben 2027 da ke tafe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp