Ganin yadda matsalar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa, Shugaban gamayyar kungiyoyin matasan arewa mazauna Legas, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci ya bayyana cewa son zuciyan wasu tsirarun mutane ne ya haddassa matsalar wadda aka kasa magancewa har yanzu a Nijeriya, musamman a yankin arewa.
Ya ce sanin kowa ne akwai matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu, wanda ya fi fice shi ne matsalar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kisan gilla da suka addabi yankin arewa maso yamma. A cewarsa, wadannan matsaloli ko shakka babu suna kara dagula ci gaban kasar nan.
Alhaji Ibrahim ya ce jami’an tsaro sun dade suna kokawa a kan yawaitar miyagun makamai a cikin kasar nan, wadanda muyagun ‘yan siyasa suke amfani da su wajen cimma burikansu da ke jefa dar-dar a zukatan jama’a.
Ya ce matsalolin tsaro suka kara ta’azzara a cikin kasar nan, kuma akwai bukatar masu ruwa da tsaki tun daga kan shugabanni da sarakuna da jami’an taro da su yi wa tukar hanci, domin duk ranar da ‘yan kasa suka fusata hankali zai tashi fiye da wanda aka gani a zanga-zangar Endsas da ta gudana a kudu.
Shugaban gamayyar ya yi kira da shugabanni da su gaggauta sayo kan matsalar tsaro a fadin kasar nan tun kafin lokaci ya kure musu, domin idan tura-ta-kai bango har har talakawa suka fusata, to abubuwa ba za su yi kyau ba.
Ya ce kashi sittin na matsalolin tsoro a kasar nan suna faruwa ne saboda rashin cika alkawura ga jama’a da shugabanni ke yi da rashin adalci da rashin tausayi na shugabanni ga talakawansu, wannan ne ya samar da rashin tagomashi na gwamnati ga jama’a, inda a yanzu an kai lokacin da mulki da shugabanci suka zama abin son zuciya, babu wanda zai iya tabbatar da cewa akasarin wadanda aka zaba su wakilci jama’a na yin hakan kamar yadda ya dace ba tare da son zuciya ba.
Daga karshe ya yi kira da shugabanci da su sani duniya ba wurin zama ba ne, kuma duk abin da suka shuka, shi ne za su girba a gobe kiyama. Ya ce idan aka cire son zuciya komai zai kawo karshe a ɓangaren matsalar tsaro.