Gwamnatin Jihar Kwara, ta koka kan rashin isassun likitoci a cibiyoyin kiwon lafiya na jihar, sakamakon yawaitar ficewar da likitocin ke yi zuwa kasashen ketare.
An bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai na farkon sulusin shekarar 2025, wanda ma’aikatar sadarwa ta shirya a Ilorin.
- Adadin Wuraren Cajin Ababen Hawa Masu Aiki Da Lantarki Na Sin Ya Karu Da 47.6% A Shekara
- ISWAP Sun Kai Hari Sansanin Sojoji A Yobe
Da yake jawabi yayin taron, Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitocin Jihar, Dakta Abdulraheem Abdulmalik ya bayyana cewa, duk da umarnin da Gwamna Abdulrahman Abdulrazak ya bayar na daukar likitoci, hukumar ta kasa samun ma’aikatan da suka cancanta da za su iya dauka aiki.
Dakta Abdulmalik ya ce, a halin yanzu gwamnatin jihar na da likitoci 99 kadai ne, wadanda ke kan tsarin albashi, ya kara da cewa; adadin da ake bukata kuma sun kai kimanin 180 zuwa 200.
“Likitoci ukun da suka bar aiki, sun dawo bayan karin albashin likitocin da gwamnan ya yi a baya-bayan nan. Don haka, a da muna da likitoci 96, amma bayan karin albashin da gwamnan ya yi, uku da suka bar aikin sun dawo. Saboda haka, a halin yanzu muna da likitoci 99. Kazalika, muna da bukatar kari, domin kuwa kimanin likitoci 180 zuwa 200 muke bukata.”
Saboda haka, hukumar ta ce; tana kokarin samar da wata manhaja da za ta bai wa marasa lafiya, domin ziyartar cibiyoyin kiwon lafiya 45 da kuma samun bayanai kan adadin likitocin da ake da su a kowane lokaci, domin rage jinkirin da aka saba samu na ganin likita.
Ya ce, hakan kuma zai rage yanayin da marasa lafiya kan samu kansu ko kuma fita daga hayyacinsu kafin su ga likita a asibiti.
Babban Sakataren ya kara da cewa, yankunan karkara su ne wuraren da kalubalen ya fi yin kamari, ya ci gaba da cewa; hukumar na aikin samar da kudaden alawus-alawus ga likitocin, domin magance lamarin da kuma samar da kayan aiki.
“Albashin zai kasance daidai da abin da ake biya a kasashen Turai, inda yawaicin likitocin ke arcewa a matsayin balaguro”, in ji shi.
Dakta Abdulmalik ya ce, akwai wani shiri da gwamnatin jihar ke yi na kokarin cike gibin da ake da shi a bangaren likitocin jihar, inda ya ce shirin zai fara nan shekara hudu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp