Iyalan maharba 16 daga Jihar Kano da aka kashe a garin Uromi, a Ƙaramar Hukumar Esan ta Arewa Maso Gabas a Jihar Edo, sun fito neman a biya su diyya kwanaki 40 bayan kisan ‘ya’yansu.
An kashe maharban ne a watan Maris yayin da suke dawowa gida domin bikin Sallah Ƙarama.
- Za Mu Magance Matsalar Ruwan Sha Kafin Ƙarshen 2025 A Kaduna – Uba Sani
- Majalisar Dattawa Ta Kafa Kwamitin Sa Ido Kan Gwamnatin Riƙo A Ribas
Maharban sun fito ne daga ƙananan hukumomin Kibiya, Rano, da Bunkure a Jihar Kano.
Iyalan sun taru a harabar sakatariyar Ƙaramar Hukumar Kibiya inda suka yi karatun Alƙur’ani domin roƙar wa mamatan rahamar Ubangiji.
Sun ce har yanzu gwamnati ba ta bayyana matakin da ta ɗauka ba, balle a yi maganar diyya ko hukunta waɗanda suka aikata laifin.
Malam Bala Dutse, wanda ɗansa Amadu yana cikin waɗanda aka kashe, ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin mantawa da al’amarin.
“An ce an kama wasu, amma har yau ba mu ji komai ba. Na rasa ɗana, kuma rayuwata ta shiga taka mai wuya. Mafi ƙaranci, gwamnati ta fito ta faɗa mana abin da ke faruwa,” in ji shi cikin hawaye.
Hauwa’u Isa, matar ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe, ta ce tana wahala da ’ya’yanta uku.
“Sun ce za su taimaka mana da adalci, amma har yau babu wani taimako. Ba zan daina fatan samun adalci ba, amma har yaushe za mu jira?” in ji ta.
Idan ba a manta ba gwamnonin Kano da Edo, Abba Kabir Yusuf da Monday Okpebholo, sun ziyarci iyalan maharban a baya, inda suka yi alƙawarin za a yi adalci da kuma ba su tallafi.
Gwamna Abba ya kafa kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam Gwarzo.
Sai dai bayan kwanaki 40, iyalan na ci gaba da kukan cewa babu wani ci gaba da aka samu.
Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kibiya, Nasiru Adam Abdulaziz, ya ce ya fahimci halin da ake ciki, amma ya roƙi su da su yi haƙuri.
Ya tabbatar da cewa an kama wasu kuma an kai su Abuja, amma ya nemi a yi shari’a a bainar jama’a domin tabbatar da adalci.
Wannan kisa ya nuna irin matsalar rikice-rikicen ƙabilanci da ake fama da ita a Nijeriya.
Da dama na ganin cewa gwamnati na yin alƙawuran da ba ta cikawa, lamarin da ke hana mutane yarda maganganunta.
Yayin da aka yi addu’ar 40 ta mamatan, iyalansu sun ce ba za su daina nema wa ’yan’uwansu adalci ba.
“Za mu ci gaba da magana har sai an yi mana adalci,” in ji Malam Bala Dutse.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp