Kafofin yada labarai na kasashen duniya sun bayyana kasuwar sayayya da yawon bude ido ta Sin a lokacin hutun ranar ma’aikata ta duniya da ta wuce a matsayin mai matukar kuzari. Alkaluman da Sin ta fitar sun shaida hakan, inda yawan tafiye-tafiyen da Sinawa suka yi a tsawon lokacin hutun ya kai miliyan 314, wanda ya karu da kashi 6.4% bisa na makamancin lokacin a bara. Yawan kudin da aka kashe kuma, ya kai dala biliyan 24.96, wanda ya karu da kashi 8.0% bisa na makamancin lokacin a bara.
Karuwar kasuwar sayayya ba ta rasa nasaba da nagartattun manufofin kasar Sin. Daga taron tattaunawa kan ayyukan tattalin arzikin Sin da kwamitin kolin JKS ya gudanar bara, zuwa rahoton ayyukan gwamnati na bana, an bayar da muhimmanci matuka ga habaka bukatu na cikin gida. Kana tun daga farkon shekarar da muke ciki, shugabannin Sin suka yi muhimman tsare tsare a wannan bangare. A farkon watanni 3 na bana, rawar da yawan sayayya ya taka ga bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya kai kashi 51.7%, adadin da ya karu da kashi 7.2% bisa na makamancin lokacin a bara. Boyayyen karfin manyan kasuwanni ya fara bayyana, duba da sauyawar salon bunkasuwar tattalin arziki zuwa dogaro da kasuwar sayayya ta cikin gida.
- Tattalin Arzikin Sin Tamkar Teku Ne Ba Karamin Tabki Ba
- Nijar Ta Soke Yarjejeniyar Tattara Bayanai Da Rasha Da Turkiyya, Ta Fara Neman Sabbin Abokan Hulɗa
Ban da wannan kuma, yawan baki daga kasashen waje da suka yi yawon bude ido a nan kasar Sin ya karu matuka duba da manufar yada zango ba tare da visa ba da ma yadda aka kyautata manufofin mayar wa baki haraji bayan komawa. Alkaluman da aka bayar na nuna cewa, a tsawon lokacin hutun, yawan yawon bude ido daga kasashen waje ya karu da kashi 173% bisa makamancin lokacin a bara. Daga “China Travel” zuwa “China Shopping”, wato abu mafi jan hankali a shafin yanar gizo dake da nasaba da kasar Sin, ya bayyana yadda Sin take kokarin bude kofarta ga ketare.
Kwatankwacin yadda wasu kasashe suka kafa shingaye da katse hulda da sauran kasashe, Sin tana kokarin habaka hadin gwiwarta da sauran kasashe da more damammaki tare, kuma hutun ranar ma’aikata ta duniya da ya shude ba da dadewa ba, ya nunawa duniya hakan. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp