A jiya ne jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai ya gana da ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar. Jakada Yu ya bayyana cewa, ganawar da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da mista Tuggar a kasar Brazil a baya-bayan nan, ta aike da sako mai karfi cewa, Sin da Najeriya na tsayawa tsayin daka kan bin ra’ayin bangarori daban-daban, da tabbatar da adalci da daidaici.
A nasa bangare, minista Tuggar, ya yi kyakkyawan nazari kan yadda huldar dake tsakanin kasashen biyu ke gudana, ya kuma jaddada cewa, Najeriya na fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin cinikayya, zuba jari, da hada-hadar kudi da dai sauransu, da zurfafa tuntubar juna da hadin gwiwa a harkokin da suka shafi bangarorin daban daban.
Bangarorin biyu sun amince cewa, daukar matakan kakaba harajin da Amurka ta yi ba bisa ka’ida ba, ya matukar yin illa ga ka’idojin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, da kuma halaltattun hakkoki da muradun dukkan kasashe. Ya kamata kasashen duniya su hada kai tare da yin adawa da dabi’ar cin zarafin da Amurka ke yi bisa radin kai. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp