Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, sun sanya hannu kan wata sanarwar hadin gwiwa, game da zurfafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani.
Cikin sanarwar wadda shugabannin biyu suka sanyawa hannu a jiya Alhamis, Sin da Rasha sun bayyana adawa ga tsarin daukar matsayar kashin kai, da aiwatar da takunkumai ba bisa doka ba, dangane da sassa da suka hada da cinikayya da hada-hadar kudi.
- Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha
- AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa
Sassan biyu sun kuma ce wasu kasashe, da magoya bayansu sun kakaba irin wadannan takunkumai, tare da kara yawan haraje-haraje, da aiwatar da wasu matakai na gogayyar ciniki da suka sabawa dokokin kasuwanci, wanda hakan ya yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya, ya illata salon gogayya ta adalci, kana ya dakile hadin gwiwar kasa da kasa a fannin warware tarin kalubalen bai daya dake addabar daukacin bil’adama, ciki har da yukurin shawo kan matsalar rashin wadatar abinci, da tsaron makamashi, da kare nasarorin da aka cimma karkashin kudurorin wanzar da ci gaba mai dorewa na MDD ko SDGs.
Sanarwar ta kara da cewa, Sin da Rasha za su ci gaba da hada hannu wajen dakile koma bayan da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, da ingiza shigar karin kasashe masu tasowa cikin tsarin cinikayyar kasa da kasa da na shiyyoyi.
Har ila yau, Sin da Rasha za su bunkasa tsare-tsare, da hadin gwiwa don tunkarar manufar Amurka ta dakile Sin da Rasha. Dukkanin sassan biyu na nuna matukar adawa da manufar tunzura wasu kasashen duniya ta yadda za su kyamaci Sin da Rasha, da shafawa hadin kan Sin da Rasha bakin fenti.
Bugu da kari, Sanarwar ta ce Sin da Rasha na goyon bayan kasancewar MDD jigo na shugabancin batutuwan da suka shafi kirkirarriyar basira ko AI, da jaddada muhimmancin martaba ikon mulkin kai na kasashe daban daban, da nacewa bin dokokin kasashe mabanbanta, da martaba ka’idojin MDD yayin gudanar da hakan. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp