Daga ranar 7 zuwa ta 8 ga watan Mayun nan, tawagar likitocin kasar Sin a kasar Saliyo karo na 26 ta shiga cikin yankunan karkara da dama na kasar Saliyo, inda ta kammala ayyuka hudu na bayar da jinya kyauta cikin kwanaki biyu, tare da bayar da hidimar jinya ga mazauna kauyakan da ma’aikatan kamfanoni.
A gun gudanar da ayyukan jinyar kyauta, kwararrun likitocin kasar Sin daga bangaren aikin tiyata na gama-gari, da aikin kasusuwa, da aikin kula da mata da na sauran sassa sun gudanar da gwaje-gwajen lafiya da gano cututtuka da kuma ba da jinya cikin tsari a wurin bayar da jinya na wucin gadi da rarraba magunguna kyauta, tare da ba da cikakken jagora kan yadda za a yi amfani da magunguna da rigakafin cututtuka. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp