Kwanakin baya ne Kwamret Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina ya rungumi wani aiki na neman farfadowa tare da bunkasa tsarin dimokradiyya a yankin Afrika ta yamma, musamman ganin wasu kasashe a yankin sun fuskanci juyin mulki inda aka halin yanzu sojoji ne suke mulki a kasashen. Kasashen da Kwamrad ya ziyarta sun hada da Ghana, Saliyo, Kodeboa, laberiya Gini da kuma kasar Mali.
A hirar da ya yi da Editanmu Bello Hamza, Kwamret Bishir Dauda ya ce, burinsa shi ne bunkasar tsarin mulkin dimokradiyya tare da tabbatar da adalci a sassan Afrika gaba daya. Haka kuma balaguron na faruwa ne a daidai lokacin da kungiyar ECOWAS ke cika shekara 50 da kafuwa. Ga dai yadda hirar ta kasance.
- Fursunoni 62 Sun Rubuta Jarrabawar NECO da MBAIS A Kano
- Shugaban INEC Ya Yi Kira Da A Sake Fasalin Tsarin Zabe Gabanin 2027
Da farko za mu so ka gabatar mana da kanka
Sunana Kwamret Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, babban Daraktan Kungiyar wayar da kan al’umma a kan yaki da cin hanci da rashawa mai suna CPAC-I a Nijeriya.
Me nene makasudin ziyarar kasashen yankin Afrika ta yamma da ka yi ta mota kwanakin baya.
Na yi wannan wannan ziyara ne saboda shaukin da nike da shi a kan abin da ya shafi kishin kasata Nijeriya, da kuma neman hadin kan kasashen Afirika ta yamma mu zama tsintsiya madaurinki daya,da son zaman lafiya da ci gaban Dimokaradiyya.
Kazalika, na yi wannan rangadi ne domin murnar cikar kungiyar ECOWAS shekara 50 da kafuwa. Kasan an kafa kungiyar ne ranar 28 ga watan Mayu,1975 bana kungiyar za ta cika shekaru 50. To kasancewa shekaru 50 sun wuce wasa na ga cewa, kungiyar ta cancanci a yaba mata, kuma a kara matakaimi da azama. Kuma za ka yarda da ni idan na ce ma cikin wadannan shekaru 50, Kungiyar ta taka muhimmiyyar rawa ta a zo a gani wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirika da hadin kai tare da kulla zumunci a tsakanin wadannan kasashe. Kadan daga cikin rawar da Kungiyar ta taka sun hada da cire bisa ga matafiya mazauna yankin, hakan ya karfafa shige da fice don kasuwanci, neman ilimi da yawon bude .
Wani kuma ci gaba da Kungiyar ta kawo shi ne samar da zaman lafiya. Mun ga rawar da Kungiyar ta taka a lokacin yakin basasa a kasashen Saliyo da Laberiya.
Haka kuma, Kungiyar tana assasa mulkin Dimokaradiyya, kamar yadda ta yi a kasashen Nijar, Gambia da Cote D’Iboire a lokutta daban-daban. To wadannan sune dalillaina na nuna goyan baya ga Kungiyar.
Ya al’ummar Kasashen suka karbi gangamin da ka kai musu na bunkasar dimokradiyya
Alhamdulillah, mutane sun ji dadi kuma sun ba da hadin Kai. Na hadu da mutane daban-daban, Kuma abin da na fahimta shi ne mutanen Afirika mutane ne masu son zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kuma mutane suna goyon bayan mulkin Dimokaradiyya.
Ta yaya Nijeriya za ta amfana da wannan ziyarar?
Nijeriya ta dade tana taka rawa wajen taimaka wa kasashen Afirika. A tsarin manufofin kasashen ketare na Nijeriya, Najeriya tana fifita muradan kasashen Afirika.
Idan aka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirika, Nijeriya za ta amfana. Ni Kuma dama manufar tattakina shi ne a zauna lafiya.
Sannan kada ka manta ko bayan cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu,shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, Nijeriya ce ke ba da kaso mai tsoka na kudaden da ake tafiyar da ECOWAS. Saboda haka, nuna goyan baya ga ECOWAS daidai yake da nuna goyan baya ga kasata Nijeriya.Wanda ba ya san ECOWAS, ba ya son Nijeriya, nima ba na son shi kowaye.
Wanne tallafi ka samu daga gwamnati a wannan gaggarumin aiki da ka yi?
Ina dai fatan yanzu gwamnati za ta tallafa mani in samu in buga littafina Mai sunan : ECOWAS: Labarin Ziyarata kasashen Afirika ta yamma. Wannan littafin ya kunshi duk abubuwan da suka shafi ziyarata wadannan kasashe goma wadanda na ziyarata ta mota. Kuma zan so in kaddamar da littafin nan ba da dadewa ba.
Ko akwai wani bayani da kake son al’umma su sani da ban tambaye ka ba?
Al’umma su daina bari ‘yan siyasa na yaudarar su. Ya kamata mutane su nemi sahihan bayanai game da mulki da tsarin mulki.
Mu daina kira wa kanmu ruwa, kamar masu da’awar mulkin soja. Mulkin soja bala’i ne ba alheri ba ne. Duk kasashen nan na AES da ake mulkin soja,suna cikin fitina. Amma sai a boye gaskiya azo ana yada farfaganda da karya. Mu son kasarmu,mu nuna kishinta, kada mu dinga aibata ta domin ba mu da wata kasar sai ita.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp