A watanni biyu da suka wuce Kauyuka a Kananan Hukumomin,a Bokkos da Bassa na Jihar Filato sun yi matukar shan wahala daga hare- haren ‘yan ta’adda, wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka da Kaddarori. Yawancin mutane sun samu raunuka lokacin hare- haren.
Jaridar mako ta Trust ta bayyana cewa makiyaya masu kiwon Shanunsu a Kananan Hukumomin Bassa, Riyom,Jos ta Kudu da Mangu suna daga cikin wadanda su ‘yan ta’addar suka yi niyyar kaiwa harin, inda rahoto ya nuna akwai zargin da ake yi na Kashe mutane,sace Shanu,da kuma sa masu guba.
- Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum 6 A Nasarawa
- ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 6 A Ƙauyukan Filato, Sun Jikkata Wasu
Halin rashin tsaron da ake ciki a yankin ya jawo hankalin manyan jami’an tsaro wadanda hakan ya sa suka kai ziyara,da suka hada da,Shugaban rundunar ‘yansanda ta kasa Kayode Egbetokun, Shugaban rundunar Soja ta kasa,Laftanal Janar Olufemi Oloyede,da kuma mai ba Shugaban kasa shawara kjan harkokin tsaro na kasa,Nuhu Ribadu,domin a gano dalilan da suka sa aukuwar rikice- rikice,hare- hare,da kuma tashe- tashen hankula.
Tashe-tashen hankula da kuma shafi al’ummomi da yawa a Kananan Hukumomin biyar na Jihar Filato da suka hada da Mangu,Bokkos,Jos ta Kudu, Riyom,da kuma Bassa, al’ummar Fulani sun nuna rashin jin dadinsu akan lamarin da suka ce babbar asara ce suka tafka cikin wata biyu daga watannin Maris zuwa Afrilu.
Kamar yadda makiyayan suka ce, daruruwan Shanunsu da Tumaki ko dai an sace su, an harbe su sun mutu, ko kuwa hakanan su ‘yan ta’addar suka zuba masu guba, ko wasu wadanda ba ‘a san su ba, daga al’ummomi masu dama a cikin Kananan Hukumomi biyar da suke Arewacin da kuma tsakiyar Jihar. Sun kara jaddada cewa sun yi asarar fiye da Naira milyan 300 na Shanu, wanda lamarin ya kara jefasu cikin babbar matsalar tattalin arziki da halin da rayuwarsu take ciki.
Shugaban kungiyar ya yi magana
Ibrahim Yusuf Babayo,Shugaban kungiyar Miyetti Allah masu kiwon dabbobi na kasa ya bayyanawa jaridar karshen mako cewar dukkan hare- haren da ake kaiwa dabbobin da kuma kashesu an sanar da jami’an tsaro daban- daban,da suka hada da Kwamanda na rundunar soja ta,3 kuma kwamandan Operation Safe Haben (OPSH), Manjo- Janar Foluaho Oyinlola,Kwamishinan‘yansanda na Jihar, Emmanuel Adesina,da kuma darekta na bangaren jami’an farin kaya DSS.
Ya ce jami’an tsaro da suke a bangaren Karamar Hukuma an kai su can wuraren da aka kai hare- haren domin su ganewa idanunsu yadda lamarin yake.
Sa Wa Shanu 110 guba
Kamar yadda jagorancin kungiyar MACBAN a Jihar yace,an kashe Shanu a kalla 110 ta hanyar guba a hare- haren da aka kai daban- daban.
Babayo ya yi zargin cewa an yi amfani ne da gauta, mangwarori da sauran kayan abinci wadanda aka zuba masu guba,aka kuma zuzzubasu wuraren da ake kiwo saboda dabbobin su ci.Ya kara da cewa masu kai harin suna sau da yawa suna zuba gubar ne wuraren da dabbobin suke zuwa domin shan ruwa.
Lokacin da aka kai hare- haren
Makiyaya a Jihar sun ce tsakanin watan Maris zuwa Afrilu 2025,an samu al’amarin da ya shafi saw a Shanu guba a wurin kiwonsu sau shida a Kananan Hukumomin Bassa da Mangu.Bugu da kari tsakanin Maris 3 zuwa 10, Shanu 9 an sa masu guba a kauyukan Kwerenkwe, Rukwechogu da kuma Dan Tanko a cikin Karamar Hukumar Bassa.
Hakanan ma ranar 31 Maris, 2025, sai kuma wasu Shanu 10 da aka sa wa guba a gundumar Woshina, Panyam ,Karamar Hukumar Mangu.Sai kuma,2 Afrilu ,Shanu 20 su ma haka aka yi masu duk dai a garin Woshina.
Makiyayan haka suka ce ranar 14 Afrilu 14, hanu 4 su ma basu tsira ba daga hakan a cattle were a a gundumar Anchetahu, Miango,a Karamar Hukumar Bassa ;bayan kwana biyu kuma,sai kuma ga wasu 36 su ma dai duk lamarin gubar ne kusa da kwanar Tafi Gana ranar 16 Afrilu 2025.
Jaridar Trust ta karshe mako ta bada labarin cewar ranar 16,Afrilu a kwanar Tafi Gana can ma din an sa wa Shanu 36 guba, mataimakin Insifekta Janar sashen ayyuka,DIG B.D Kwazhi,wanda aka maida shi Jihar domin ya kawo zaman lafiya tsaknain al’ummar Jihar,ya ziyarci wurin da lamarin ya faru cikin rakiyar Kwamiushinan ‘yansanda na Jihar,sashen Jihar Filato ranar 17 Afrilu domin su jajantawa wadanda aka sa wa Shanun nasu guba.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansanda ta Jihar DSP Alabo Alfred,a wata sanarwar da ya fitar bayan ziyarar 17 Afrilu da ya kai a wurin da lamarin ya faru, ya lura da cewar Shanun 33 an sa masu guba ne har sai da suka mutu,na wadansu mutane ne wadanda har yanzun ba a gane ko su wanene ba daga wurin,ya lokacin da ya kai ziyara wurin, mataimakin Insifekata Janar na ‘yansanda,DIG ya ja kunnen su makiyayan da,cewar kada sukai ramuwar gaiya.
Hakanan ma ranar 18 Afrilu, 2025, Gwamnatin Filato ta hannun Kwamishinan yada labaranta, Joice Ramnap,ya kafa kwamiti domin ya binciki lamarin. Kwamishinan ya ce Gwamna Caleb Mutfwang ya ba ma’aikatar ci gaban dabbobi da lamauran lafiyarsu da Kifi, su yi cikakken bincike dangane da zargin da ake yi.
Ranar 22 Afrilu, duk dai Jaridar ta bada rahoton an sa ma Shanu 36 guba kusa da ofishin Hukumar Zabe mai zaman kanta a Karamar Hukumar Mangu lokacin da suke kiwo a wurin, inda ya kara da cewa Jami’in ‘yansanda na wurin (DPO), shiyya ta 8 Kwamandan Operation Safe Haben, da kuma wanda ke kulawa da ofishin Hukumar farinkaya sun je wurin domin su ganewa idanunsu abubuwan da suka faru.
A wancan harin ta’addancin da aka kai wani mutum mai suna Alhaji Nyako Muhammad,wanda shi makiyayi ne,ya yi bayanin yadda ransa ya baci inda yace lamarin ya jefa iyalansa cikin matsalar koma-baya,inda kuma yake bayanain cewa,“wadanda suka aikata laifin sun sa wa mangwaro guba inda aka zube su kasa.Sai dai kuma wani abin bakin- ciki dabbobinmu sunci magwarorin,da aka sa wa guba. Dukkannin jami’an hukumomin tsaro na Karamar Hukumar tare da Shugaban Karamar Hukumar sun sann halin da ake ciki da kuma abubuwan da suka faru.
Ya ce sa wa Shanu na guba gaba daya abin ya shafi hanyoyin da iyali na suke samun yadda za su tafiyar da rayuwarsu“.Shanun sun kai Naira milyan 33 yawancinsu na marayu ne a karkashin kulawa ta. Sune muka sa ran a kansu wajen tafiyar da harkokinmu.Fiye da mutane 20 sun dogara ne kan Shanun ,yanzu kuma sai ga shi duk an kashe su.Mun ja hankalin matasa cewar kada su yi ramuwar gaiya. Muna yin kira ga gwamnati ta shiga cikin lamarin namu kamar yadda ya ce’’.
Ismail Idris,wanda shi ma makiyayi ne da ya rasa Shanunsa 36 ta hanyar gubar da aka sa masu kusa da kwanar Tafi Gana cewa yayi kudin Shanun sun kai Naira milyan 23.
Ya ce“Ban san abinda zan yi ba.Asarar da na yi tayi yawa.An lalata mani hanyar tafiyar da rayuwata.Ina da yara ; babu wani abinda na sani in ban da kiwon Shanu kamar yadda ya jaddada,”.
Harbe Shanu 45
Al’ummar da yawansu makiyaya ne sun bayyanawa Jaridar Trust ta karshen mako cewa an kasha Shanu 45 ne a garuruwan Tangjol da Tashek cikin Karamar Hukumar Riyom, yayin da sauarn an kasha su ne a , kauyen Shen,Karamar Hukumar Jos ta Kudu.
Shi kuwa Abdullahi Garba, Shugaban Jiha na kungiyar ci gaban Gan Allah Fulani (GAFDAN), ya bayyana cewa ranar 19 Afrilu,2025,an harbi Shanu f4 su kuma masu kiwonsu an ji masu rauni,a Tangjol, cikin Karamar Hukumar Riyom.Har ila yau ya kara da cewa ranar 27 Afrilu 2025 an kara kashe Shanu 37 .
Makiyayan sun ce ranar 21 Afrilu, 2025, ‘yan ta’adda sun kashe Shanu 3 da kuma makiyayi daya,Hamza Suleiman a kauyen Shen, cikin Karamar Hukumar Jos ta Kudu.
Bashiru Haruna, wanda shi ma makiyayi ne ya yi asarar Shanu 37 lokacin da aka yi harbe- harbe,a garin Riyom, ya ce kudin Shanun sun kai fiye da Naira milyan 30 sanadiyar shi hari na harbe- harben da aka kai.
“Dukkan Shanun shikenan sun tafi na rasa su.Kowane daya daga cikin manyan ba zai rasa kai kasa da Naira milyan1 ba.Gaba daya, asarar ta kai ta fiye da Naira 30,amma sai ‘yan ta’addar suka kasha su,basu barni da komai ba.
“Wannan lamarin ya jefa iyalaina cikin halin rudani. Kiwon Shanu shi nake yi domin tafiyar da rayuwata. ‘Ya’yana basu kammala makaranta ba, maganar ma su samu ayyukan yi daga gwamnati bata ma taso ba, domin su kula da iyali.Gidan mu yanzu babu komai hanyar da muke amfani wajen tafiyar da rayuwarmu yanzu babu ita an raba mu da ita kamar yadda ya yi karin bayani”.
Sace Shanu 206
Al’ummar wuraren da ake yin kiwo wato makiyaye sun yi zargin sace masu Shanu lokacin da aka kai hare- haren.
Shugaban kungiyar masu kiwon Shanu MACBAN na Jihar Filato ya ce ranar 2 ga Maris 2025,an sace fiye da Shanu 30 a Marish cikin Karamar Hukumar Bokkos.
Hakanan ma makiyayan su zargi cwa ranar 13 ga Afrilu 2025, an sace Shanu 30 yayin da shi makiyayin babu wanda ya san inda yake a garin Murish karkashin Karamar Hukumar Mangu.
Bugu da kari kumaan bayyanawa Jaridar karshen mako duk dai a rana daya, an samu labrin sace Shanu 14 wadanda suke mallakin wani mutum ne da ake kira Salihu Amadu,a kusa da Kopgain, a gundumar Langai da ke karkashin Mangu.
Hakanan ma ranar 22 Afrilu 2025,an sace Shanu, 132 kusa da garin Jwokshang,a Karamar Hukumar Mangu da wata kungiyar mahara ‘yanta’adda suka yi .
Shagari Manu,wanda shi ma lamarin sace Shanun ya shafe shi a Mangu,yace Shanu 170 da kudinsu ya fi Naira milyan 100 wadanda mallakin shi ne da shi da dan’uwansa an sace su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp