Babban da ga shahararren jarumin fina-finan Hausa Rabilu Musa Ibro, wanda Allah ya yi wa rasuwa shekaru 9 da suka gabata, Hanafi Rabilu Musa Ibro ya bayyana yadda har yanzu suke amfanuwa da zaman arziki da mahaifinsu ya yi da mutane a lokacin da yake raye, Hanafi wanda shima ya shiga harkar barkwanci ya kuma bayyana cewar duk da cewar mahaifin nasu ya dade da rasuwa amma har yanzu mutane suna ci gaba da yi masa addu’oin samun rahamar Ubangiji.
Hanafi a wata hira da ya yi da BBC Hausa ya ce sau da dama a kan kirashi a wata harkar samun kudi kokuma a yi mashi alheri sai ace wannan abin da muka yi maka saboda mahaifinka ne, a lokuta da dama mu kan ji ko kuma a fada mana cewar mahaifinmu ya samu kyakkyawan yabo a wajen mutanen da ya yi mu’amala dasu da kuma wadanda yake sakawa nishadi, a farkon rayuwata ban sa ran zan yi wani aiki na fim ba.
- Jajircewa Ce Sirrin Samun Daukakata A Masana’antar Kannywood -Sadik Sani Sadik
- Kallo Daya Mutum Za Yi Min Ya Gane Masana’antar Kannywood Ta Canza Rayuwata -Farida Abdullahi
Amma bayan rasuwar mahaifina sai naga mutane na ta yabonsa su na yi mashi shaidar ayyukan alheri, sai na yanke shawarar tsunduma harkar ka’in da na’in don kuwa mu an mutu an bar mana gadon abin alheri, duk yanda mutum ke ji da gadon da aka bar mashi a gida nima haka nike jin wannan gadon sana’a da mahaifina ya rasu ya bar mani inji Hanafi.
Hakan kuma yana matukar yi mana dadi, domin babu abinda yafi a yi wa wani naka fatan alheri ko bayan ransa in ji Hanafi, yanzu haka nine Kansila na Wucin Gadi a gundumar Danlasan da ke Qaramar Hukumar Warawa da ke nan Jihar Kano kuma ni dalibi ne a FCE Kano inda nike karatun B.Ed amma nikan samu saukin yin wasu al’amuran sakamakon yadda wasu ke taimakona ta sanadiyar mahaifina inji shi.
Ya kuma kara da cewa har yanzu mu da muke ‘ya’yansa mukan samu wata alfarma a sanadiyarsa, domin a wasu lokutan akwai wuraren da ban kai in shiga wajen ba, amma saboda kasancewata dansa sai a barni in shiga ba tare da wani shinge ko kyara ba, hakan ya sa muke matukar godiya da yadda mutane ke saka shi a cikin addu’oinsu a kowane lokaci, kuna muna fatan Allah SWA ya kyautata makwancinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp