A Yau Lahadi, da misalin karfe 3:15 na yamma, za a sake gwabzawa a wasan karshe tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa na Real Madrid da Fc Barcelona (El classico) na wannan kakar, masana nan ganin cewa, wannan wasa tamkar bugun karshe ne na cikin kofi a tsakaninsu.
Wannan bai rasa nasaba da tarihi da kuma kwarewa a taka leda da duka kungiyoyin biyu ke da shi, Real Madrid da Barcelona sun shafe tsawon lokaci su na gabar kwallo a tsakaninsu, sun yi manyan ‘yan wasa sun kuma lashe manyan kofuna da duk wata kungiya ke fatan lashewa a kwallon kafa.
- UEFA: An Kai Ruwa Rana Yayin Da Inter Ta Koro Barcelona Gida
- Barin Liverpool Ita Ce Shawara Mafi Wahala Da Na TaÉ“a Yankewa A Rayuwata -AlexanderÂ
Wasan na yau shi ne na hudu da kungiyoyin suka hadu a bana, wasan farko da aka buga shi ne wasan Mako na 11 na gasar Laliga inda Barcelona ta doke Real Madrid da ci 4-0, sai wasa na biyu shi ne wasan karshe na kofin Spanish Super Cup wanda shina Barcelona ta doke Madrid da ci 5-2.
Wasa na uku da kungiyoyin suka hadu a bana shi ne wasan karshe na kofin Copa Del Rey inda nan na Barcelona ta sake samun nasarar doke Madrid da ci 3-2, a wannan karon kocin Madrid Carlo Ancelotti na fatan ganin kungiyarsa ta samu nasara akan Barcelona duba da cewar wannan ka iya zama wasan karshe da ita a matsayinsa na kocin Real Madrid.
Manyan yan wasan da bazasu buga wannan wasa sakamakon raunin da suka samu sun hada da Joules Kounde da Pablo Torre a bangaren Barcelona, sai kuma Antonio Rudiger, Eduordo Camavinga da Ferlnad Mendy a bangaren Real Madrid.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp