Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar a Rasha ta kara yaukaka cikakkiyar huldar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani tsakanin sassan biyu, kuma ta yi tasiri wajen hade tafiyar sassan kasa da kasa a fannin wanzar da oda tsakanin kasashen duniya bayan aukuwar yaki, da ingiza tasirin sassa daban daban a harkokin duniya, da sake gina kyakkyawan tsarin siyasar duniya.
Wang Yi, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na jiya Asabar, ya ce bisa gayyatar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi masa, shugaba Xi ya gudanar da ziyarar aiki a Rasha, tare da halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar babban yakin kare kasa na tsohuwar tarayyar Soviet tsakanin ranakun Laraba zuwa Asabar.
- Minista Ya Ƙaddamar Da Yekuwar Wayar da Kan Ɗalibai Kan Kafofin Sadarwa
- 2027: Har Yanzu Ba Mu Saka Ranar Fara Sabunta Katin Zabe Ba — INEC
Yayin ziyarar, shugaba Xi tare da takwaransa na Rasha sun gudanar da zuzzurfar tattaunawa game da batutuwan da suke jan hankalinsu a tsawon kusan sa’o’i 10, kuma sakamako game da batun siyasa mafi jan hankali da aka cimma sanadiyyar ziyarar, shi ne sanya hannu da shugabannin biyu suka yi kan takardar hadin gwiwa, don zurfafa cikakkiyar huldar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani tsakanin sassan biyu.
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya kara da cewa, halartar bikin nasarar da tsohuwar tarayyar Soviet ta samu a ranar Jumma’a 9 ga watan nan da shugaba Xi ya yi, ya sake tabbatar da aniyar kasar Sin ta yin aiki tare da sauran kasashe, wajen tabbatar da hakikanin abubuwan da suka faru yayin yakin duniya na 2, da burin hadin kai don kare odar kasa da kasa bayan yaki.
Kazalika yayin ziyarar, shugaba Xi ya kuma yi cudanya da jagororin siyasa daga kasashe daban daban, wadanda suka halarci bukukuwan da suka gudana, tare da gudanar da taruka da manyan shugabannin duniya daga nahiyoyi 3, inda suka cimma matsaya mai ma’ana dangane da goyon bayan juna, da kare salon cudanyar mabambantan sassa, da nuna adawa da siyasar nuna karfin tuwo da cin zali. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp