A yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, Sin da Amurka sun cimma matsaya tare da fitar da sanarwar hadin gwiwa bayan taron kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, inda ya kara da cewa, hakan wani muhimmin mataki ne da bangarorin biyu suka dauka na warware sabaninsu ta hanyar yin shawarwari da tuntuba bisa daidaito, tare da aza tubali da samar da yanayi na kara dinke baraka da zurfafa hadin gwiwa.
Daga bangarenta kuwa, Darakta-Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, a jiya Lahadi ta bayyana cewa, ta yi farin cikin ganin an samu sakamako mai kyau yayin taron kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Okonjo-Iweala ta ce tattaunawar ta nuna wani muhimmin mataki na ci gaba, inda ta kara da cewa bisa halin da ake ciki a duniya, irin wannan ci gaba da aka samu na da matukar muhimmanci ba ga kasashen biyu kadai ba, har ma da sauran kasashen duniya, ciki har da kasashe masu fama da matsalar tattalin arziki. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp