ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Aikin Yi: A Halin Yanzu Masu Digiri Na Sayar Da Fiya Wata Da Aikin Achaba

by Idris Aliyu Daudawa
10 months ago
Aiki

Yawancin wadanda suka kammala jami’oi a Nijeriya suna yin wasu kananan ayyuka ko sana’oi wadanda idan da ace akwai ayyukan yi wadanda suka fi su ba za su taba yin su ba, musamman ma idan aka yi la’akari da wahalhalun da suka fuskanta kafin su kai ga kammala karatu, hakan shi yasa suka hira da wakilan jaridar LEADERSHIP inda suka yi bayanai na yadda suke fuskanta matsin rayuwa :sun bayyana dalilan da suka sa suke yin ayyukan; me ya kai ga har, sa su yanke shawarar yin hakan, wace irin dadewa suka yi suna tafiyar da ayyukan, da kuma irin yadda muatne suke kallonsu saboda aikin nasu.

EBONYI: A Jihar Ebonyi wadanda suka kammala jami’oi suna aiki ne Hotel inda suke aikin bada barasa wato giya, ‘yan Okada, da kuma masu tuka Keke Napep.

  • Ana Fatan Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
  • A Karo Na Hudu ’Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Sun Yi Nasarar Kammala Ayyukansu A Wajen Kumbon

A, Abakaliki hedikwatar Jihar Ebonyi da wasu garuruwa na kewaye da ita an lura da cewa yawancin wadanda suka kammala jami’oin sun samu kansu ne cikin kananan ayyuka wadanda idan ba domin rayuwa ce ta canza ba, kuma samun aikin yana da wuya, hakan ce ta sa su, kamar wadanda suna aiki a Hotel domin kai Barasa ga wadanda suke bukata, masu kula da wuraren ajiye kaya, Okada, da kuma yaron mota wanda zai rika yi, A hirar da suka yi da LEADERSHIP ta Lahadi sun bayyana cewa sun yanke shawarar da su yi ire- iren ayyukan ne saboda ko ba komai za su samu abubuwan da za su rika cin abinci, su kula da kannensu, da kuma Iyaye, bugu da kari kuma, domin su kaucewa irin tunanin nan da zai sasu, aikata laifukan da basu da kyau kamar, Karuwanci, da kuma sauran ayyukan da basu dace ba ace ana aikata su.

ADVERTISEMENT

Mace da ta kammala jami’a ta karanta lamarin daya shafi aikin Jarida a Jami’ar Jihar Ebonyi (EBSU) , Miss Ifeanyinwa Oforbiike, wadda ita ma tana aiki ne a Hotel a matsayin mai raba Barasa a wani katafaren Otel Abakaliki, tace ana biyanta alabashin Naira30, 000 kowane wata ta yi dana-sani domin kuwa kamar yadda tayi bayani aka share wata uku zuwa hudu, kafin abiyata albashin wata daya a matsayin daga cikin bashin da take bi.

Tace bayan kammala karatunta ta nemi aiyukan yi daban- daban, ta bangaren hukumomin gwamnati da kuma na masu zaman kansu, sai dai kash! ba ta, samu nasara ba kamar yadda ta jaddada.

LABARAI MASU NASABA

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa

“Daga baya kuma sai ta fada cikin lamarin yin Takalma, sai dai abin ban takaici, ba tada isassun kudaden da za su taimaka mata don sabuwar harkar yin Takalma sana’ar da tasa kanta. Tana fatan idan ta samu isassun kudade, za ta sake komawa harkar.”

Miss Oforbiike ta kara yin bayanin ta hadu da abubuwan takaici, an maida ta wata ba kome ba, sai bakaken maganganu da ta fuskanta lokacin da take tafiyar da harkar.

Mista Celab Ogodo ya ce ‘Ina samun kudade da yawa ta hanyar tuka KekeNapep fiye da ma’aikatan gwamnati’

Ya kammmala karatunsa ne daga Kwalejin ilimi ta Jihar Ebonyi, ya ce shi bai dauki aikinsa kamar wanda bai dace ba, domin kullum yana samun Naira 15,000 bayan wasu kudaden da ya kashe.

AKWA IBOM: Wadanda suka kammala jami’a suna aiki kamar, Direbobin motar daukar fasinja, da kuma saayar da Kifi

Duk da Jihar tana daga cikin Jihohin da suke samar da Manfetur a Kudu maso Kudu, wadanda suka kammala Jami’oi suna tafiyar da rayuwarsu ta kudaden da suka samu ta hanyar kananan ayyukan da basu samun kudaden da za su ishe su tafiyar da rayuwa, irinsu suna da yawa a Jihar ta Akwa Ibom, musamman ma zirga – zirga, bangaren shari’a, sana’ar da bata taka kara ta karya ba a harkar ruwa, a wuraren da suke kusa da ruwa.

Wasu daga cikinsu,wadanda suke harkokin zurga- zurga domin samun abin rufawa kai asiri, sun bayyana wahalhalun da suka sha, bayan kammala karatun jami’a fiye da shekara 10 “amma babu wani ci gaban da ak samu.”

Ekene Stephen, shi ya karanta Philosophy ne kamar yadda ya ce: “Na kammala Jami’ar UYO tun shekarar 2011, amma har yanzu ban samu wani aiki mai nagarta ba.Na yi kokarin samun aikin gwamnati matsayin Malamin makaranta, amma har yanzu ban samu ba. An dauke ni aikin Malamin makaranta mai zaman kanta a God’s Power International School, amma albashi Naira 35,000 ne suke bani.

 

BENUWE:

A Jihar Benuwe, wasu daga cikin wadanda suka kammala Jami’a suna tuka Okada ne da kuma sayar da ruwan fiyo water da snack, domin kawai su samu damar na abinci da sauaran wasu abubuwa.

A tattaunawar da aka yi da shi, Ijiir-Iter Thomas, da ya kammala karatu, ya kuma karanta Geography daga Jami’ar Jihar Benuwe, 2007 ya ce tun da ya gama aikin yiwa kasa hidima (NYSC), ya nemi bukatar daukje shi ayyuka daban daban ciki da wajen Jihar, amma bai samu sa’ar samu ba, don haka ya yanke shawarar ya fara, da sayar da snacks (shawarma) a bakin titi, sana’ar daya koya a sansanin masu yiwa kasa hidima.

 

Kamar yadda ya ce da farko, naji tsoron irin maganganun da mutane za su yi – Dan Okada

 

RIBAS: Wadanda suka kammala Jami’a suna sana’ar sayar da manfetur a gidajen mai da kuma Malamai a makarantu masu zaman kansu.

Yawancin wadanda suka kammala Jami’a a Jihar Ribas suna yin wasu ayyukan da wasu kudade ake samu masu yaw aba, abinda ya fara daga msu sayar da man fetur a gidajen mai, da kuma kasancewa masu gadi, wadanda za su rika canjin iki saboda su rika zuwa aiki a makarantu masu zaman kansu.

Da take hira da Jaridar LEADERSHIP ta karshen mako, Ifeoma Cletus, da ta karanta Philosophy, tana koyarwa ne a wata makaranta mai zaman kanta a Fatakwal, tace rashin samun aikin ya sa ta yanke shawarar aikin koyarwa.

 

KADUNA:

A jihar Kaduna wasu daga cikin wadanda suka kammala Jami’a wadanda suka zanta da LEADERSHIP ta krshen mako sun bayyana rashin ingantattun ayyuka, da kuma irin matsin tattalin arzikin d ake fuskanta yanzu, na daga cikin manyan dalilan da suka sa su shiga irin su ayyukan da suke yi, domin kawai su samu damar tafiya da rayuwa, Wadanda suka kammala jami’a suna yin aiki ne a matsayin masu shara da goge a Otel ko kuma sana’ar Okada.

Mark Bala ya karanta Turanci ne a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, shi ma shi yake tukawa domin ya rufawa kan sa asiri abinda aka fi sani da Okada Rider, cewa ya kwashe shekara shida yana neman aiki amma bai samu ba.

Ya ce “Bayan ya kammala yiwa kasa hidima, a shekarar 2019, Ina nemi ayyukan yi, daga gwamanti da kuma wurare masu zaman kansu ba tare da ya samu ba. Ni yanzu mai sana’ar Okada ne.Ina ci da kaina da kuma iyalina, a a halin yanzu wannan shi ne aiki na. Wani lokaci na kan koma gida da Naira ku san 10,000 kowace rana bayan idan akwai gyare- gyare da kuma sayen mai.”

 

DELTA: Wadanda suka kammala jami’a suna aikin gyran mota, masu hana hatsaniya a gidajen shakatawa (Otel) da kuma kashe Beraye

Lokacin da Kareem Usman ya iso, birnin Benin, a shekarar 2015 bayan ya kammala yiwa kasa hidima, ya yi tsammanin ai shi zai samu kwanciyar hankali. Bayan shekarun da yayi na karade Nijeriyta wajen neman aiki, aiki da Kamfanin tayis na Chaina a gundumar Utesi a lokacin yana yiu ma kan sa kallon babu wanda ya fi shi sa’a.

“Ya zo birnin Benin ne saboda yayi aiki da Kamfanin Chaina wanda yake yi tayis,” ya tuna da wata ganawar da aka yi ma shi. “Kamfanin yana gundumar Utesi ne.”

Amma kuma daga baya sai farincikin da yake da shi ya koma bakin ciki.

“Saboda albshin bai taka kara ya karya bane ba zai ishe shi yin wani abu ba,” kamar yadda ya bayyana.“Ya yi shekara biyar kafin ya bar wurin. Saboda wurin da ya yi aiki idan ya yi kwana biyar bai je aiki ba, shikenan ya rasa albashin watan ke nan.”

 

ANAMBRA: Wadanda suka kammala jami’a suna aikin direbobin motocin fasinja da masu lura cunkoson abubuwan hawa

Chidiebere Chibueze, mai shekara 31, da Chioma Ifediorah suna daga cikin wadanda suka kammal akaratun Jami’a masu yawa a Awka, Jihar Anambra , wadanda dole ce ta sa, su ayyukan da suke yiu yanzu domin neman su tsira da mutuncinsu.

Yayin da Chibueze ya yi karatuns a a Jami’ar Jihar Imo 2015 da digirin din lamarin kasuwanci, Chioma ita kuma ta kammala Jami’ar Azikiwe Unibersity (UNIZIK), a Awka, shekarar 2009 da digiri din yadda za’a tafiyar da harkokin kudi.

Aiki
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Sarakunan Da Suka Yi Wa Turawan Mulkin Mallaka Turjiya A Nijeriya
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Yajin Aiki: Ƙungiyar Likitocin Nijeriya Ta Ba Gwamnati Wa’adin Mako Huɗu

MASU ALAKA

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya
Rahotonni

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

July 14, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Rahotonni

Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa

July 11, 2026
Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

June 26, 2026
Next Post
Ilimin Fasaha Shi Ne Tafarkin Cire Nijeriya Daga Kangin Fatara – NBTE

Ilimin Fasaha Shi Ne Tafarkin Cire Nijeriya Daga Kangin Fatara – NBTE

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.