China da Amurka sun cimma matsaya na rage harajin da suka ɗora wa kayayyakin juna, a wani mataki da ake sa ran zai taimaka wajen rage tashin-tashinar kasuwanci da ta shafi tattalin arziƙin duniya tun a shekarun baya.
Sanarwar ta fito ne bayan wata muhimmiyar tattaunawa da wakilan ƙasashen biyu suka yi a birnin Geneva na ƙasar Switzerland, kuma hakan ya zo wa da dama a matsayin abin mamaki, musamman ganin yadda rikicin kasuwancin ke tsakanin ƙasashen biyu tun dawowar Shugaba Donald Trump kan mulki.
- Sin Ta Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Da Ake Iya Sarrafawa Daga Nesa
- Kaico: Wani Ƙani Ya Kashe Saurayin Yayarsa A Kano
A cewar bayanan, Amurka ta yadda za ta rage harajin da ta ɗora a kan kayayyakin da ke shiga daga China daga kashi 30 cikin 100 zuwa ƙasa.
A gefe guda kuma, China za ta saukar da nata harajin daga kashi 25 cikin 100 zuwa kashi 10 cikin 100 a kan kayayyakin Amurka.
Wannan yarjejeniya za ta fara aiki daga ranar Laraba mai zuwa, kuma za a kwashe kwanaki 90 ana aiwatar da ita a matsayin gwaji.
Idan aka ga tana da tasiri, ana iya tsawaita ko kuma daidaita matakin.
Masana tattalin arziƙi sun bayyana cewa wannan ci gaba zai iya taimakawa wajen farfaɗo da cinikayya tsakanin manyan ƙasashen biyu, kuma zai taimaka wa ƙasashe masu tasowa da ke dogara da su wajen kasuwanci da kayan masarufi.
Rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China ya fara ne tun daga 2018 lokacin da kowanne ɓangare ke ƙara haraji a kan kayayyakin juna, lamarin da ya haifar da hauhawar farashi da rikicin masana’antu a duniya.
Matakin rage harajin da suka ɗauka yanzu na iya zama sabon shafi na fahimtar juna da haɗin gwiwa a tsakanin manyan ƙasashen biyu na duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp