A yau Talata ne aka gudanar da bikin bude taron ministoci karo na 4 na dandalin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean wato CCF, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarta tare da gabatar da jawabi.
A cikin jawabinsa, Xi ya ce, Sin da kasashen Latin Amurka suna hadin kai wajen kafa kyakkyawar makomar al’ummunsu na bai daya, Kana Sin na fatan kara hada hannu da kasashen Latin Amurka a bangarori 5, don samun bunkasa tare, duba da cewa manufar kare kai da kariyar ciniki suna kara kunno kai.
- Ya Kamata Amurka Ta Daina Yin Barazana Da Matsin Lamba Idan Tana Son A Tattauna Batun Harajin Kwastam
- Rikicin Ribas: Fubara Ya Ce Ya San Yadda Zai Magance Matsalar, Ya Gargaɗi Magoya Bayansa
Wato na farko, a bangaren hadin kai, Sin na fatan bangarorin biyu za su taimakawa juna a muradu masu tushe, da batutuwan dake jawo hankalinsu.
Na biyu, samun ci gaba, wato ya kamata bangarorin biyu sun kara tuntubar juna ta fuskar manyan tsare-tsare, da gaggauta raya shawarwar “Ziri Daya da Hanya Daya” mai inganci.
Na uku, al’adu, Sin na fatan hada hannu da kasashen Latin Amurka wajen tabbatar da shawarar wayewar kan duniya, ta yadda za a kafa ra’ayi mai adalci, da koyi da juna da fahimtar juna.
Na hudu, zaman lafiya, Sin na fatan tabbatar da shawarar tsaro ta duniya tare da bangaren Latin Amurka, kuma za ta samar musu horo a bangaren aiwatar doka da shari’a bisa bukatunsu.
Na karshe, muradun jama’a, inda karkashin haka Sin za ta samarwa dalibai 3500 na mambobin kawancen kasashen Latin Amurka wato CELAC tallafin kudin karatu cikin shekaru 3 masu zuwa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp