Rundunar ‘yansandan Jihar Kogi, ta kama mutane 239 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Miller Dantawaye, ne ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar da ke Lokoja a ranar Talata.
- Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban APC A Ondo, Sun Nemi N100m
Ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka kama, 66 ana zarginsu da aikata fashi da makami, 75 satar mutane, sannan 18 kuma da kisan kai.
Haka kuma, ya ce an kama mutane 21 da ake zargi da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, wasu 21 da an zarge su da aikata fyaɗe, guda shida an zarge da aikin asiri, da kuma wasu 49 da ake zargi da aikata wasu manyan laifuka.
‘Yansanda sun kuma ƙwato makamai da yawa.
Makaman sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda biyar, AK-49 guda biyu, harsasai sama da 400 da sauransu.
CP Dantawaye, ya ce rundunar ta fara horar da jami’anta domin ƙara musu ƙwarewa da ƙaimi wajen yaƙi da laifuka kamar garkuwa da mutane da fashi da makami.
Ya ce wasu jami’an da suka halarci wani horo na musamman sun kammala a makon jiya, sannan kuma rundunar ta ƙaddamar da sabbin dabarun yaƙi da laifuka kamar sintiri a manyan hanyoyi, kai samame maɓoyar ‘yan daba, da kuma binciken motocin jama’a a wurare daban-daban.
Ya ƙara da cewa rundunar tana aiki da al’umma ta hanyar amfani da tsare-tsaren ‘yansanda.
Kwamishinan ya buƙaci al’ummar Jihar Kogi, musamman sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ƙungiyoyin matasa da sauran masu ruwa da tsaki, da su ba mi wa ‘yansanda goyon baya domin a samu zaman lafiya da tsaro a jihar.
Ya roƙi haɗin kan jama’a don kare rayuka da dukiyoyinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp