A jiya ne uwar gidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan da matar shugaban kasar Brazil Rosângela da Silvaa wadda ta rako mai gidanta a ziyarar da yake yi a kasar Sin, suka ziyarci babban zauren nuna fasahohin nishadantarwa ta kasar Sin, inda suka kalli abubuwan dake ciki, tare da kallon wasan opera da wasu wake-waken Sin da Brazil.
Peng Liyuan ta bayyana cewa, Sin da Brazil suna mu’amala da juna a fannin al’adu, kuma jama’ar kasashen biyu suna ta kara fahimtar juna, da sada zumunta mai zurfi. A nata bangare kuwa, Madam Rosângela ta jinjinawa nasarorin ci gaba da kasar Sin ta samu da kuma yadda ake raya al’adun kasar. Tana fatan kara sa kaimi ga yin mu’amala a tsakanin kasashen biyu a fannin al’adu, da kuma ci gaba da bayar da gudummawarta ga zurfafa zumunta a tsakanin kasashen biyu. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp