A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Colombia Gustavo Petro, wanda ya zo birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, domin halartar taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean wato CCF.
Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da Colombia wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, tare da daga hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi, ta shigar Colombia cikin shawarar “Ziri daya da hanya daya”.
- Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja
- JAMB: Tangarɗar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025
A nasa bangare kuwa, shugaba Petro ya bayyana fatan yin hadin gwiwa da kasar Sin, wajen kare yanayin adalci na duniya, da kuma kiyaye moriyar kasashe maso tasowa yadda ya kamata.
Haka kuma, A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Chile Gabriel Boric, wanda ya zo birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, domin halartar taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean wato CCF.
Yayin tattaunawarsu Xi Jinping ya ce kasar Sin tana son karfafa fahimtar siyasa a tsakaninta da kasar Chile, da nuna goyon baya ga juna kan harkokin dake shafar mihimmiyar moriyar kasashen biyu. Kasar Sin tana goyon bayan kamfanonin kasar da su zuba jari a Chile, kana tana son shigo da kayayyakin Chile masu inganci kasar Sin.
A nasa bangare kuwa, shugaba Boric ya ce, kasar Sin ta kasance abokiyar ciniki mafi muhimmanci ga kasarsa, kuma hadin gwiwarsu ya ba da tallafi ga al’ummomin kasashen biyu. Kazalika kasar Chile tana fatan yin hadin gwiwa da Sin wajen kare dangantakar cude-ni-in-cude-ka da kiyaye karfin MDD, tare da kuma kare yanayin adalci na kasashen duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp