Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ce ƙungiyar ECOWAS na dab da rushewa saboda rashin nagartaccen shugabanci, rashin yarda tsakanin shugabanni, da raunin cibiyoyi.
Ya bayyana haka ne a ranar 9 ga watan Mayu, 2025, a Jami’ar Oxford, yayin taron cika shekara 50 da kafuwar ECOWAS.
- ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME
- Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa
Gwamna Bala ya ce akwai babban koma-baya a fannin shugabanci a ƙasashen yammacin Afirka, kuma hakan yana shafar rayuwar jama’a ta yau da kullum.
Ya ce rashin shugabanci mai kyau da cibiyoyin da ba su da ƙarfi su ne manyan matsalolin da ke hana ECOWAS aiki yadda ya kamata.
Ya bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu a Bauchi, musamman a fannin ilimi, lafiya, ababen more rayuwa, da tallafin tattalin arziƙi, a matsayin hujja cewa shugabanci nagari yana iya kawo ci gaba.
Tsohon Shugaban Ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, wanda shi ma ya gabatar da jawabi a taron, ya goyi bayan maganar Bala Mohammed.
Ya ce rashin yarda da haɗin kai tsakanin shugabannin ƙasashe yana durƙusar da ECOWAS.
Obasanjo ya kuma bayyana damuwarsa game da sabuwar ƙungiyar Alliance of Sahel States (AES) da Mali, Nijar da Burkina Faso suka kafa.
Waɗannan ƙasashe da dakarun soja ke mulki, sun bayyana ficewarsu daga ECOWAS.
Taron da aka gudanar a Oxford ya tattaro shugabanni, jakadu da masana domin tattaunawa kan dimokuraɗiyya, tsaro da cigaban yankin yammacin Afirka.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mukhtar Gidado ya fitar, ya bayyana halartar Gwamna Bala a taron a matsayin alamar tasirinsa a yankin, da kuma jajircewarsa wajen ganin ECOWAS ta zauna lafiya da ci gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp