• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Jagoranci Taron Manyan Wakilai Game Da Nazarin Matakan Aiwatar Da Manufofin Taron Ministocin FOCAC Na 8

by CMG Hausa
3 years ago
Wang Yi

Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya karbi bakuncin taron manyan wakilai, game da nazarin matakan aiwatar da manufofin taron ministocin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC karo na 8.

Wang Yi, wanda ya jagoranci taron na jiya Alhamis ta kafar bidiyo, ya ce
taron ministocin FOCAC da ya gudana a birnin Dakar na kasar Senegal a watan Nuwambar 2021, ya aza wani ginshiki mai karfi game da alakar Sin da kasashen nahiyar Afirka.

  • Sin: Hadin Gwiwar Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ta Haifar Da Sakamako Mai Kyau Da Fa’ida

Ya ce yayin bikin bude taron na Dakar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana burin kasarsa na yin aiki tare da kasashen Afirka wajen aiwatar da muhimman ayyuka 9, matakin da ya yi matukar samun karbuwa, a matsayin wanda zai bunkasa ci gaban kasashen Afirka, tare da daga matsayin hadin gwiwar sassan 2.

Wang ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka sun yi aiki tare, wajen shawo kan wahalhalu da kalubale, suna kuma aiki kafada da kafada, wajen aiwatar da sakamakon taro na 8 na ministocin kasashen dandalin FOCAC.

Ya ce bayan taron, Sin da kasashen Afirka sun samu manyan nasarori, tare da samun moriya cikin gaggawa, a fannin shawo kan kalubalen karancin abinci, da magance annobar COVID-19, da bunkasa ci gaba mai dorewa, tare da ingiza zaman lafiya da daidaito.

LABARAI MASU NASABA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Ministan wajen na Sin ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, tare da gabatar da wasu shawarwari na tabbatar da nasarar gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani.

Taron dai na wannan karo, ya samu halartar ministoci daga kasashen Senegal, da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Libya, da Angola, da Habasha, da Masar, da Afirka ta kudu, da kuma wasu karin wakilai daga hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU.

Har ila yau, taron ya amince da sanarwar manyan jami’an zaman, game da aiwatar da manufofin taron ministocin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC karo na 8. (Mai Fassarawa: Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
Next Post
Gwamnati Tarayya Ta Rufe Kamfanonin Takin Zamani 4 A Kano

Gwamnati Tarayya Ta Rufe Kamfanonin Takin Zamani 4 A Kano

LABARAI MASU NASABA

Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025
Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.