Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bayyana muhimmancin amfani da karfin tattalin arzikin kasar da ci gaba mai dorewa da yake samu, wajen rage radadin rashin tabbacin da ake fuskanta a duniya da inganta dauwamammen ci gaba mai inganci a kasar.
Li Qiang ya bayyana haka ne jiya Alhamis, yayin taron majalisar gudanarwar kasar kan habaka tattalin arziki, wanda ya gudana karkashin jagorancin mataimakin firaminista Ding Xuexiang.
- A Tsammaci Garambawul Ga Dokar Zabe Kafin Zaben 2027 — Shugaban INEC
- Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci
Li Qiang ya ce ya zama wajibi kasar Sin ta hada aikin bunkasa bukatu a cikin gida da zurfafa gyare-gyare a tsarin samar da kayayyaki da kuma karfafa hada kasuwar cikin gida da ta ketare.
Domin bunkasa tattalin arzikin kasar, firaministan ya nanata bukatar mayar da hankali kan bangarori kamar na inganta ware dukkan nau’ikan albarkatu ga bangarorin da suka dace da tabbatar da hada kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da kirkire-kirkiren bangaren ayyukan masana’antu, da gina cikakken tsarin gudanar da ayyukan masana’antu, da samar da kayayyaki mai dogaro da kansa, da kuma tabbatar da daidaito tsakanin bukatu da samar da kayayyaki, yayin da dukkansu ke samun sauye-sauye.
Ya kuma bukaci a yi kokarin tallafawa kamfanonin kasar masu fitar da kayayyaki, da daidaita batun samar da aikin yi, da kara habaka sayayya da zuba jari, domin tabbatar da samun ci gaba da wadata.
Firaminista Li ya nanata cewa, ya kamata dukkan sassan gwamnati da larduna su karfafa tsara manufofi da aiwatar da su, da inganta hadin gwiwa, domin kyautata kuzarin kasuwa da warware matsalolin al’umma yadda ya kamata. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp