‘Yan bindiga sun saki karin wasu mutane hudu daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da suka sace a ranar 28 ga watan Mayu, 2022.
Daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da wata mata mai shekaru 85, Hajiya Halimatu Atta da diyarta mai shekaru 53, Adama Aliyu.
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Saki Karin Mutane 4 Na Jirgin Kasan Abuja-Kaduna
- Gwamnatin Nijeriya Na Kashe Naira Biliyan N18.397 Kullum A Bangaren Tallafin Mai
Wanda ya jagoranci sulhun sakin fasinjojin, Tukur Mamu, ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa an sako mutanen ne da yammacin ranar Juma’a bayan shafe sama da watanni hudu a hannun wadanda suka sace su.
A halin da ake ciki, Mamu ya ja hankalin gwamnatin tarayya da kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), game da shirin da ‘yan ta’adda suka yi na aurar da ‘yar karamar yarinya, Azurfa Lois John mai shekaru 21 a duniya, kamar yadda suka yi wa Leah Sharibu a Jihar Yobe a shekarun baya.
A cewar Mamu, daya daga cikin manyan kwamandojin ‘yan ta’addan an ce yana soyayya da Misis John.
Sai dai ya yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki da su kara zage damtse wajen ganin an sako mutanen 23 da har yanzu suke tare da ‘yan ta’addan wadanda yanayin lafiyarsu, a cewarsa, na da matukar tausayi da bukatar kulawar gaggawa.
Mamu ya kuma yi kira ga kungiyar CAN da kada ta sanya siyasa a lamarin, ko kuma ta mayar da shi zuwa ga sanarwar manema labarai kawai, amma da ta hada kai da hukumomin da abin ya shafa don jawo masu garkuwa da mutane kan lamarin Misis John tun kafin lokaci ya kure.