Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar wa al’ummar Zamfara ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya kuma mai rahusa a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Asabar yayin da yake ƙaddamar da Babban Asibitin Anka da aka gyara da kuma aka saka kayan aiki na zamani.
- Gidauniyar Mangal Ta Dauki Nauyin Yi Wa Mutum 12,300 Masu Cutar Kaba Aiki A Katsina
- Bude Kofar Kasar Sin Dama Ce Ga Duniya Har Abada
Gyaran Babban Asibitin Anka ya haɗa da tsohon sashen mahukunta asibitin, ɗakunan kwantar da marasa lafiya maza, ɗakunan kwantar da marasa lafiya mata, ɗakin bada magani, sabon get don tsaron asibitin, zauren da ya haɗe ɗakin mata, sashen X-ray da ɗakin tiyata, da sabon ginin sashen kula da haɗari da rashin lafiya na gaggawa, ɗakin gwaje-gwaje, sashen kula da ido da haƙori, da sashen mata masu juna biyu da tsohon ɗakin gwaje-gwaje.
Sauran sassan da aka gyara da kuma saka kayan aiki sun haɗa da sashen Kulawa da Mata (ANC), ɗakin tiyata, ɗakin X-ray, sabon ginin hukunta asibiti, masallaci, gidan Babban Daraktan Lafiya (gidaje mai ɗakuna 3), da kuma sashen kula da yara, da dai sauransu.
A yayin jawabinsa a wajen ƙaddamar da aikin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, an kammala gyaran gine-ginen tare da sanya dukkan kayan aikin kiwon lafiya cikin kwangilar cikin watanni 12.
Gwamnan ya ce, “A shekarar da ta gabata ne aka fara gyaran wannan asibitin, kuma wani kamfanin cikin gida ne aiwatar da kwangilar.
“Saba hannun jarin ya mayar da asibitin zuwa wurin kiwon lafiya na zamani tare da na’urori na zamani, wannan ba shakka zai inganta jinya ga ‘yan jihar a garin Anka da kewaye.
“Ga al’ummar Anka da kewaye, wannan aiki na ɗaya daga cikin alƙawuran da muka ɗauka na samar da ribar dimokuraɗiyya da inganta rayuwar ‘yan ƙasa.
“Za mu ci gaba da ba da fifiko kan al’amuran ci gaba, tare da tabbatar da cewa al’ummarmu sun samu ingantaccen lafiya kuma da araha, ilimi, noma, hanyoyi, da sauran muhimman ababen more rayuwa a faɗin jihar nan.
“Zuwa ga ma’aikata da mahukuntan babban asibitin Anka, ina kira gare ku da ku tabbatar da gudanar da wannan cibiya mai inganci da kulawa, ina kuma roƙon ku da ku jajirce wajen samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga jama’armu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp