Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin ɗaukar nauyin Hajjin iyalan Falasɗinawa 1,000 da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza da Isra’ila.
Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin.
- Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha
- Isra’ila Ta Yi Barazanar Kai Hare-Hare Kan Iran Kamar Hamas Da Hezbollah
Sarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke ciki sakamakon yaƙi da ƙasar Yahudawa ta Isra’ila ta ƙaddamar a Gaza.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp