Da yammacin jiya Litinin, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci birnin Luoyang na lardin Henan.
A yayin ziyarar, Xi ya ziyarci kamfanin Bearing Group na Luoyang, da gidan ibada na “Farin Doki”, da kuma ramin dutse na Longmen.
- Hajji: Kawo Yanzu An Kammala Jigilar Maniyyatan Jihohi 12 A Nijeriya – NAHCON
- ’Yansanda Sun Kama Wani Mutum Sanye Da Kayan Mata A Coci A Adamawa
Ya fahimci yadda aka inganta ci gaban masana’antun samar da kayayyaki a wurin, da karfafa kiyayewa, da amfani da abubuwan tarihi da al’adu, da habaka ingantattun masana’antun al’adu da yawon shakatawa da sauransu.
Yayin da ya ziyarci kamfanin Bearing Group na Luoyang, ya leka sashen masana’antar fasahar zamani ta kamfanin, da duba tsarin samarwa mai amfani da kirkirarriyar basira, da kuma tattaunawa tare da ma’aikatan kamfanin.
Xi Jinping ya ce, dole ne mu ci gaba da inganta masana’antar kere-kere, da tsayawa tsayin daka kan dogaro da kanmu, da mallakar manyan fasahohin zamani, da sa kaimi ga hade tsarin samarwa, koyo da kuma bincike, da bunkasa samar da dimbin kwararru masu inganci, ta yadda kasar Sin za ta iya cimma zamantarwa iri ta salon Sin ba tare da kama hannun yaro ba. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp