Rundunar ‘Yansandan Babban Birnin Tarayya, Abuja ta kashe wani riƙaƙƙen ɗan fashi da makami, mai suna Abdulmininu Bello wanda aka fi sani da Babanle.
Ana zargin Babanle da jagorantar wata ƙungiyar masu fashi da makami da satar motoci a Abuja da kewaye.
- DSS Ta Cafke Ɗan Bindiga Yayin Da Yake Shirin Tafiya Aikin Hajji A Sakkwato
- Rasha Ta Ce Za Ta Tattauna Da Ukraine Don Yin Sulhu Game Da Yaƙin Da Suke Tafkawa
Kakakin rundunar ‘yansandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce jami’ai ns musamman na rundunar da ake kira ‘Scorpion Squad’ ne suka jagoranci wannan samame.
Ta bayyana cewa tun da daɗewa rundunar ta sanya wannan ƙungiya cikin jerin waɗanda ta sanya wa ido a kansu saboda yawaitar laifuffukan da ake danganta da su.
A cewarta, jami’an tsaro sun samu bayanan sirri cewa ‘yan fashin na shirin kai hari yankin Maitama a ranar 19 ga watan Mayu, 2025.
Bayan haka, ‘yansanda sun hanzarta daƙile harin, inda suka kama su a ranar 15 ga watan Mayu, 2025.
Da ‘yan fashin suka hango ‘yansanda, sai suka fara harbi.
A lokacin musayar wutar ne, Babanle ya mutu.
‘Yansanda sun kama sauran tawagar ƙungiyar guda bakwai a wajen.
Wasu daga cikinsu tsoffin fursunoni ne, yayin da ɗaya daga cikinsu fursuna ne da ya tsere daga gidan yari.
Hakazalika, ‘yansanda sun ƙwato wasu kayayyaki ciki har da mota ƙirar Toyota Camry, babur ƙirar boxer, harsasai, bindigogi ƙirar AK-47 da kuma wata bindiga ƙirar gida.
SP Adeh, ta ƙara da cewa shugaban ƙungiyar, Solomon Bawa wanda aka fi sani da Fasto Mogu, ya tsere tare da wani mutum bayan sun samu rauni.
Ta roƙi jama’a da su sanar da ‘yansanda idan sun ga wani da raunin harbin bindiga.
Ta ce duk waɗanda aka kama suna hannun ‘yansanda, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp