Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nanata kwarin gwiwa matuka kan bunkasa ci gaba mai inganci da ingantaccen tsarin shugabanci a kasar, yayin da yake kira ga lardin Henan ya rubuta wani sabon babi a kokarin da ake na daukaka zamanantar da kasar Sin.
Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin rangadin da ya yi a biranen Luoyang da Zhengzhou dake lardin a jiya Litinin da yau Talata.
A jiya da rana, shugaban ya ziyarci rukunin kamfanin Bearing, inda ya ce, wajibi ne a ci gaba da kera kayayyaki yadda ya kamata, wanda shi ne muhimmin ginshikin tattalin arzikin kasa yayin da take daukaka zamanantar da kanta.
Ya ce, aikin kere-kere na zamani ya dogara ne kan karfafa bangaren kimiyya da fasaha, inda ya yi kira da a kara kokarin samar da nasarori a bangaren fasaha, da neman cin gashin kai a bangaren kirkire-kirkire.
Haka kuma, shugaban ya ziyarci gidan ibada na White Horse, wanda aka gina a daular Donghan, inda ya aka masa bayani game da yadda aka rungumi addinin Buddha mai salon kasar Sin da kuma kokarin da ake yi na kare kayayyakin tarihi a wurin.
A ziyarar da ya kai jerin kogon Longmen, mai shekaru sama da 1,500 wanda UNESCO ta sanya cikin jerin wuraren tarihi da aka gada na duniya, wanda kuma shi ne ke wakiltar matsayin koli na fasahar sassaka kan dutse ta kasar Sin, shugaban ya bayyana muhimmancin karewa da gado da ma yayata al’adun gargajiya na kasar Sin masu daraja. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp