Jama’a masu bibiyarmu a wannan shafi mai matuKar farin jini ina muku sallama irin ta Addinin Musulunci Assalamu alaikum wa rahmatullah.
Da fatan kuna cikin Koshin lafiya. A wannan makon za mu fara kawo muku tsaraba ce daga irin launukan da ya dace a Kawata falo da su a zamanance.
Na san yana daga cikin burin kowace mace ta ga ta tsara falon gidanta yadda duk wanda ya gani zai yi sha’awa musamman maigida ran gida.
Launin Kore (Green), Launin Toka-toka (Grey), da Launin Kakin Sojojin Ruwa su ne suka zama mashahurai da ake amfani da su wajen Kawata falo a wannan zamanin.
Sabon bincike na Shafin Swyft Home, ya gano cewa jama’a masu son ado sukan yi zabi mafi dacewa a abubuwa da yawa na rayuwarsu musamman batun launuka na kaya ko fentin gida da za su Kawata gidajensu su yi kyau da sha’awa.
Ba abin mamaki ba ne cewa launin toka ya kasance mai farin jini na biyu baya ga Kore da ya sha gabansa, yayin da sauran wasu launukan kamar bulu su ma suka kasance masu ba da sha’awa. Sai dai duk da cewa launin Kirim (Cream) da Fari (White) ba su yi wani farin jini na a-zo-a-gani ba zuwa yanzu a shekarar nan ta 2022 (kamar yadda masana kwalliya suka yi hasashe), ruwan hoda da rawaya kuwa, sun samu Karin karbuwa.
“Kore (Green) shi ne launin da aka fi yayi a falo tun daga farkon shekarar 2022, don haka ya zama a matsayi na daya saboda yadda ake neman sa don Kawata launin falo,” in ji Ben White, masanin kwalliya da kasuwanci a shafin Swyft Home.
“An yi hasashen farin jinin da launin kore zai yi a tsakanin masana kwalliya da masu Kwata adon gida tun kafin shekarar 2021, don haka ya zama shi ake yi a yanzu wajen Kawata falo don ya yi kyawon gani. Ina ga abin da ya sa launin kore ya samu irin wannan karbuwa da farin jini shi ne, akwai mutanen da suke son ganin launin waje (na shuke-shuke da ciyayi) ya shigo cikin gidajensu.”
“Hada launuka masu ban sha’awa da Kayatarwa shi ne babban abin lura wajen Kawata gida a wannan shekarar.
Shi ya sa masana kwalliya suka fi mayar da hankali a kan hade launukan da za su fi dacewa da juna a tsakanin fentin da za a yi wa falo da kayan da za a zuba a falon kamar kujeru da sauransu don falon ya zama ya tsaru yadda ya kamata.” In ji shi.
Akwai dai launuka guda 10 da za mu kawo muku su daya-bayan-daya da ake yayi wajen Kawata falo a zamanin nan.
Don haka mu hadu a mako mai zuwa domin ganin, shin wadanne launuka ne wadannan?
Mun samo daga: https://www.countrylibing.com/uk/