Akwai Kananan sana’o’i masu sauKin yi da yawa musamman ga wanda yake neman na dogaro da kai, wanda daya daga cikin su ita ce sana’ar sayar da Data wato (Reselling) a turance.
Wannan sana’an ana yin ta ne da kudi kadan don yawanci mutane sun dauka sana’ar nan sai da kudi da yawa kana iya farawa da kudi kamar dubu uku idan dai kana da waya har ma idan ka ga dama kana iya hadawa da tura ma mutane katin waya wato BTU.
Yanayin jarin da zaka fara.
Kana iya farawa da ko da Naira 3000 dubu uku ne ko kuma abin da ya wuce haka duk yadda ka ga dama kake son ka fara kuma akwai riba sosai duka misali a MTN za ka saya akan Naira 250 ka sai da 1gb zuwa Naira 300 ko kuma 350 ka ga ka samu ribar Naira 50 ko kuma Naira 100, ya danganta ga yanayin yadda wurinku ake sai da Datar.
Sai kuma a fannin katin waya na turawa za’a sai da maka akan Naira 97 ka sai da zuwa Naira 100 ka ga na dubu Naira 30 kenan shi kati bai kai Data riba ba kamar dai yadda aka san kasuwarsa.
Sauran abubuwan da za ka yi sun hada da printing na katin waya, sai kuma irin ‘Subscription’ ka na iya yi mass nan take ta hangar amfani da wayanka.
Data Flex
Data flex wata website ce mai zaman kanta wanda idan ka yi rajista da su za ka iya sayar da Data akan farashi mai sauKi, kuma ya danganta akan yadda kake son ka zuba kudin farawa wato jari wadanda suke da kamfani sun taimaka sosai saboda kusan ba ka da buKatar a ce ka zuba kudade da yawa sun lalace.
Haka ma kana da damar sayar da abubuwan kamar su kati ka na iya biyan bills kamar na wuta, Startime da sauransu ta hanyar amfani da su.
Domin farawa dole sai ka yi rajista ka na iya zuwa ta google play store domin fara Sana’a.
Akwai wani application ma da ake kiran clubkonnect idan ka je google play store.
Idan ka je google play store ka sauke manhajar, sai ka yi register za ka yi ‘activating’ ba tare da ka biya kudin rajista ba.
Idan ka shiga za ka ga abubuwan da za ka iya yi kala- kala kaman ‘Funding wallet’ wato saka kudin da za ka sayi abubuwa kamar sayen Data, sayen airtime, sayen subscription kamar su startimes, gotb da sauransu kuma a farashi mai rahusa.