Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta samu nasarar tarwatsawa da wargaza wuraren haɗawa da rabar da taki na bogi guda uku a jihar Bauchi tare da kamo kayayyakin da ake amfani da su wajen haɗa takin na bogi.
A wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar a ranar Laraba, ya ce, sun yi amfani da wani rahoton sirri da suka samu a ranar 10 ga watan Mayu wajen kai samamen.
- Sin Ta Fitar Da Fim Dake Bayyana Al’amaru Na Gaske Bisa Taken “Gajimare A Doron Kasa”
- Raya Kasa Na Bukatar Bin Daidaitacciyar Hanya
Jami’an sintiri na rundunar sun kai ga kama wani mutum Muhammad Abubakar a gidansa da ke Magaji Quarters Bauchi ɗauke da buhun taki na bogi da aka sarrafa guda 6 da kwalaben maganin ciyawa guda 46.
A wani bincike da aka gudanar a gidansa da ke unguwar Magaji Quarters, an gano katan 38 da babu kowa a ciki na maganin ciyawa iri-iri, buhunan NPK guda 14, buhunan Indorama guda 9, jerikan cokali guda biyar, murhun gawayi, daurin ledoji, da buhunan da ke ɗauke da Ztars da garin lambda.
Yayin da ake masa tambayoyi, Abubakar ya yi iƙirarin cewa makwancinsa, Abubakar Umar, shi ma na da hannu a lamarin.
A ranar 14 ga watan Mayu, bayan wani rahoto na daban, ‘yan sanda sun kai samame a wani shago da ke kan titin Gombe a cikin garin na Bauchi mallakin wani Anas Abubakar mai shekaru 32. An same shi da buhunan 44.5 na gurɓataccen taki
Da ya ke fuskantar tambayoyi, Anas ya amsa cewa na samun kayan kaolin da yake amfani da shi wajen haɗa gurɓataccen taki daga wajen wani mai suna Abdulrahaman Muhammad, ɗan shekara 24 mazaunin unguwar Bakaro.
Kazalika, jami’an ‘yansandan sun cigaba da zurfafa bincike inda hakan ya kai su ga kamo wani mai suna Ziya’u Bala, ɗan shekara 27 a duniya mazaunin unguwar Gudum Hausawa, wanda ya yi rakiya wa jami’an zuwa wanin wurin da ake aikin haɗa taki ba bisa ƙa’ida a rugar Natsira da ke ƙauyen Kangere. Wurin mai ɗauke da buhu kusan 100 na gurɓataccen taki.
‘Yansandan sun kamo buhun jabun taki guda 44, buhun kaolin guda 100, buhun taki 12, da buhun taki urea.
Wuraren hada jabun takin guda biyu da Sama’ila Abdullahi, da Mujahid Abdullahi suke gudanarwa a Natsira da Kangere duk an gano su.
Duk wanda ake zargi sun ce suna haɗa takin ne tare da sayar ma wani Abdulrahaman, inda shi kuma yake kaiwa ga Anas.
Dukkanin wuraren hada takin na jabu guda uku an tarwatsa da kamo kayayyakin da suke amfani da su wajen haɗa gurɓatattun taki.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi CP Sani-Omolori Aliyu, ya tabbatar da aniyar rundunar na gudanar da masu irin wannan aika-aikar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp