Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP na shure-shuren mutuwa ganin yadda jam’iyya mai mulki ke samun tagomashi.
Da yake jawabi a wajen taron jam’iyyar APC na kasa da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis, Ganduje, ya ce ta hanyar salon siyasar APC, jam’iyyar mai mulki za ta lashe zaben gundumomi na babban birnin tarayya (FCT) mai zuwa.
- Darussan Koyi Daga Salon Bunkasa Kasa Na Sin
- Ingancin Tattalin Arzikin Sin Mai Bude Kofa Na Bayyana Sosai Duba Da Yawan Zuwan Baki Masu Sayayya
Ya ce, saboda rigingimu da sauya sheka da suka addabi jam’iyyar PDP, “yanzu jam’iyyar ta fara jin ƙamshin mutuwa, shi ya sa da yawa daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar suka koma APC”.
Ganduje ya ce, baya ga samun nasara a jihohi 22 a cikin 36 da ke kasar nan, karin gwamna daya na kan hanyarsa ta komawa jam’iyyar nan ba da dadewa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp