An gudanar da taron kolin bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari na duniya na shekara ta 2025 jiya Alhamis 22 ga watan nan a Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
A gun taron, mai taken “rungumar zamanin digital, da samar da ci gaba cikin hadin-gwiwa”, an yi musanyar ra’ayi mai zurfi, tare da cimma matsaya daya kan batutuwa da dama, da bullo da shawarar Beijing ta taron kolin bunkasa kasuwanci da zuba jari na duniya na shekara ta 2025, inda aka yi kira da a fadada hadin-gwiwa a zamanin da muke ciki, da nufin samar da ci gaba da wadata tare.
- Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Samun Ci Gaba Mai Inganci Ta Fuskar Raya Wayewar Kai
- Dan Asalin Jihar Kano Ya Kafa Tarihin Kirkirar Manhaja Mai Auna Tsayin Bishiya A Faransa
Abubuwan dake cikin shawarar sun hada da, kafa tsarin hadin-gwiwa na zamani, don tabbatar da tsarin masana’antu, da na samar da kayayyaki yadda ya kamata a duniya, da raya yanayin yin kirkire-kirkire dake bude kofa ga kowa, da kara kawo sauki ga harkokin kasuwanci da zuba jari na duniya, tare da bunkasa fasahar kirkirarriyar basira ta AI, don ta amfani kowa da kowa, da makamantansu.
Wakilai sama da 800 daga hukumomin gwamnati, da kungiyoyin kasa da kasa, da kungiyoyin kasuwanci, da cibiyoyin raya kasuwanci da kamfanoni sun halarci taron kolin na bana. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp