Hukumomin shirya jarrabawar kammala sakandire, WAEC Da NECO Sun Saki Sakamakon Jarabawar Ɗaliban Zamfara Na Shekara Biyar, Yayin Da Gwamna Lawal Ya Warware Bashin Da Gwamnatocin Baya Suka Riƙe
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya warware dukkan basussukan da gwamnatocin baya da suka riƙe wa hukumomin jarabawa.
- Shekaru 10, Kofuna 16 Kevin De Bruyne Ya Yi Bankwana Da Manchester City
- Firaministan Sin Ya Shugabanci Taro Kan Masana’antu Masu Amfani Da Makamashi Mai Tsafta Da Kare Muhalli
Gwamnatocin Zamfara da suka shuɗe sun gaza biyan Hukumar Jarabawa ta Ƙasa (NECO) daga 2014 zuwa 2018 da Hukumar Jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) daga 2018 zuwa 2022.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa hukumomin da ke kula da jarabawar sun fitar da duk sakamakon da jarabawar da WAEC da NECO suka riƙe wa ɗalibai daga 2018 zuwa 2022.
Sanarwar ta kara da cewa, ƙoƙarin da gwamnati mai ci ke yi na warware basussukan da ake bin jihar wani bangare ne na dabarun da gwamna Lawal ya ɗauka bayan kafa dokar ta-baci kan ilimi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ƙoƙarinsa na yin garambawul a fannin ilimi a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya biya duk wani bashi a bangaren ilimi da gwamnatocin baya a jihar suka ƙi biya
“Rashin biyan kuɗin jarabawar WAEC da NECO ya haifar da koma-baya ga makarantun gwamnati a faɗin jihar Zamfara, wanda hakan ya sa Zamfara ta kasance a baya a fannin ilimi a faɗin Nijeriya.
“Da sanin matsalolin da ke tattare da harkar ilimi, Gwamna Lawal ya kafa dokar ta-baci a fannin ilimi a watan Nuwamba 2023, matakin da ya samar da sakamako mai kyau ga bangaren ilimi a jihar Zamfara.
“Sama da makarantu 500 ne aka gyara tare da samar da kayan aiki tun bayan sanarwar ta gaggawa, an kuma horar da malaman gwamnati kuma har yanzu ana ci gaba da horar da su.
“Biyan bashin WAEC da NECO cikin gaggawa zai kwantar da hankulan ɗaliban Zamfara da aka riƙe da sakamako, inda suka kammala jarabawar ƙarshe amma ba su samu damar ci gaba da karatu ba, sakamakon hana su takardar shaidar kammala jarabawar.
“Ga Hukumar Jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC), Gwamna Dauda Lawal ya biya bashin Naira Biliyan Ɗaya da gwamnatocin baya suka riƙe daga 2018 zuwa 2022.
“Gwamnatin da ta shuɗe ba za ta iya biyan kuɗin jarabawar WAEC na 2023 ba, don haka babu wata makarantar gwamnati a jihar Zamfara da ɗalibanta suka samu damar rubuta jarabawar, amma an biya kuɗin ne a shekarar 2024, kuma ɗalibai sun zana jarabawar.
“A bangaren Hukumar Shirya Jarabawar ta Ƙasa (NECO) kuwa, Gwamna Lawal ya biya bashin N320,699,850.00 da gwamnatin baya ta riƙe daga 2020 zuwa 2021.
“Gwamnatocin da suka gabata a shekarar 2014, 2015, 2016, 2017, da 2018 sun gaza biyan hukumar shirya jarabawa ta ƙasa (NECO) naira biliyan ɗaya da miliyan ashirin da biyu, dalilin da ya sa hukumar ta yanke shawarar hana sakamakon ɗaliban Zamfara da suka zauna a wancan lokacin.
“Gwamna Dauda Lawal ya kuma amince da biyan bashin sakamakon da aka riƙe daga shekarar 2014 zuwa 2018, kuma an cimma yarjejeniya da NECO inda ta fitar da sakamakon nan take bayan an biya kashi na farko na kuɗin.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp